Bayan gurfanar da su, an baiwa yan zanga-zangan EndSARS 40 da aka kama beli

Bayan gurfanar da su, an baiwa yan zanga-zangan EndSARS 40 da aka kama beli

- Masu zanga-zangan sun gurfana gaban kotu hukunta masu saba dokar COVID-19

- Baya sauraron bayanansu, kotun ta basu beli

- Manyan lauyoyi a Najeriya sun yi Alla-wadai da abinda hukuma tayi

Shahrarren dan wasan barkwanci, Debo Adebayo, wanda aka fi sani da Mr Macaroni ya samu beli tare da sauran mutane 39 da aka kama don suna zanga-zanga a Lekki Toll gate.

Lauyan matasan #EndSARS, Moe Odele, ta bayyana hakan a shafinta na Tuwita.

"Masu zanga-zangan da aka kama sun samu beli har da Mr Macaroni," Moe Odele ya bayyana.

Ta kara da cewa an caji masu zanga-zangan ne kan laifin bada dokokin COVID-19 da kuma saba umurnin haramta yin zanga-zanga.

Dukkansu sun ki amincewa da laifin da ake zarginsu dake, lauyan tace.

DUBA NAN: Rijista: Dino Melaye ya caccaki mambobin APC kan shirin sabonta rijistar jam’iyyar

Bayan gurfanar da su, an baiwa yan zanga-zangan EndSARS 40 da aka kama beli
Bayan gurfanar da su, an baiwa yan zanga-zangan EndSARS 40 da aka kama beli Credit: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA NAN: Sakamakon rikicin Yarabawa da Hausawa, Gwamnan Oyo ya saka dokar ta baci a jihar

Kun ji cewa ‘yan sanda a jihar suka kama wasu masu zanga-zangar #OccupyLekkiTollGate.

Masu zanga-zangar sun mamaye harabar tollgate ne domin yin gangamin kin amincewa da karbo wajen da kamfanin Lekki Concession Company (LCC) tayi.

Ku tuna cewa tollgate ta zamo kara zube ba tare da masu kula da ita ba tun lokacin da lamarin harbi tsakanin rundunar sojin Najeriya da masu zanga-zangar ya wakana a ranar 20 ga watan Oktoba 2020.

Sai dai kuma, a kwanan ne Kwamitin bincike na shari'a kan rikicin #EndSARS ya amince da bukatar kamfanin LCC na karbar ragamar kula da wurin.

Hakan ya fusata masu zanga-zangar #EndSARS lamarin da ya haifar da wani zagaye na zanga-zangar da aka yiwa lakabi da #OccupyLekkiTollGate.

Source: Legit.ng

Online view pixel