Yanzu-yanzu: Sakamakon rikicin Yarabawa da Hausawa, Gwamnan Oyo ya saka dokar ta baci a jihar

Yanzu-yanzu: Sakamakon rikicin Yarabawa da Hausawa, Gwamnan Oyo ya saka dokar ta baci a jihar

- Bayan rashin akalla rai guda, an garkame kasuwa Shasha dake garin Ibadan

- Rikici ya barke tsakanin kabilu biyu a ranar Juma'a kan rashin sabani

- Sakataren yada labaran gwamnan ya bayyana cewa an sanya dokar ta baci

Biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin Hausawa da Yarabawa a kasuwar Shasha dake karamar hukumar Akinyele Ibadan a jihar Oyo, gwamnatin jihar ta bada umurnin garkame kasuwar har sai lokacin da hali yayi.

Kasuwar ShaSha na daya daga cikin wuraren da ake kai amfanin gona daga Arewa, a Ibadan.

A jawabin da sakataren yada labaran gwamnan, Taiwo Adisa, ya saki ranar Asabar, ya ce gwamna Seyi Makinde ya bada umurin kulle kasuwar domin kwantar da kuran.

Hakazalika ya kafa dokar ta baci a Shasha da kewaye.

An sanya dokan ta baci ne daga karfe 6 na yamma zuwa 7 na yamma.

KU DUBA: Zulum ya baiwa Likitan da cigaba da aiki a asibitin Munguno duk da yayi ritaya kyautan sabuwar Mota

Yanzu-yanzu: Sakamakon rikicin Yarabawa da Hausawa, Gwamnan Oyo ya saka dokar ta baci a jihar
Yanzu-yanzu: Sakamakon rikicin Yarabawa da Hausawa, Gwamnan Oyo ya saka dokar ta baci a jihar Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU DUBA: Gwamnan jihar Bauchi mashirmanci ne, dan rikici ne, bai cancanci mulki ba, Gwamnan Ondo

Jawabin yace: "Mai girma gwamna Seyi Makinde, ya bada umurnin garkame kasuwar Shasha da gaggawa sakamakon rikicin da ya barke a wajen."

Gwamnan ya amince da sanya dokar hana fita a Shasha. Daga karfe 6 na yamma zuwa 7 na safe."

"Ana kira ga mazauna yankin su cigaba da harkokinsu a lokutan da aka amince a fita."

"Duk wanda aka kama yana tayar da tarzoma zai fuskanci fushin hukuma."

Tuni kun ji cewa mutum daya ya riga mu gidan gaskiya a ranar Juma'a sakamakon rikici da ta barke tsakanin Yarbawa da Hausawa mazauna garin Sasa da ke Ibadan a jihar Oyo.

An kuma kone gidaje tare da bannata dukiyoyi a rikicin da kawo yanzu ba a tabbatar da abinda ya yi sanadinsa ba, The Cable ta ruwaito.

Yan kasuwa a kasuwar Sasa, da ake sayar da tumatur da sauran kayan miya ba su samu idon sayar da kaya a yau ba saboda barkewar rikicin.

Jami'an yan sanda da na Amoketun sun isa wurin domin tabbatar da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel