Babu inda aka kai Najeriya garkuwa da mutane a yankin Sahel, Masari

Babu inda aka kai Najeriya garkuwa da mutane a yankin Sahel, Masari

- Gwamnan jihar Katsina ya jaddada maganan El-Rufa'i cewa babu hadin kai tsakanin gwamnonin Arewa

- A cewar Masari, Najeriya ta fi dukkan sauran kasashen dake makwabta arziki

- Masari ya jaddada maganar Ganduje cewa daga kasashen ketare makiyaya ke zuwa Najeriya

Gwamnan Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bayyana cewa Najeriya ce kasar dake gaba a yankin Sahel inda ake garkuwa da mutane don amsan fansa.

Gwamnan ya yi alhinin matsalar tsaron da ya addabi Arewa maso yammacin Najeriya da ma kasar ga baski daya.

Masari, wanda yayi jawabi a wani taron wayar da kai kan tsaro ga Limamai da Malaman addini a jihar ranar Asabar, ya ce masu garkuwa da mutane sun shigo Najeriya daga kasashen ketare, Thisday ta ruwaito.

Yace: "Najeriya ce kasa mafi arziki cikin kasashen yankin Sahel. Saboda haka dukkan masu harkar garkuwa da mutane da sayar da bindigogi sun mayar da hankalinsu kan Najeriya saboda a nan zasu iya sace mutum su samu N10,000,000, N50,000,000, har N100,000,000.”

KU KARANTA: Dan ta'adan ISIS ya kashe abokansa yan ta'adda 21 cikin kuskure yayin tafiya kai harin kunar bakin wake

Babu inda aka kai Najeriya garkuwa da mutane a yankin Sahel, Masari
Babu inda aka kai Najeriya garkuwa da mutane a yankin Sahel, Masari
Source: Depositphotos

Ya ce kisan mutane da garkuwa da su ya zama ruwan dare a Najeriya kuma ya kamata kowa ya hada hannu domin dakile hakan maimakon dogara kan jami'an tsaro.

A cewarsa, "Ko shakka babu kasar nan na fuskantar matsalolin tsaro. Duk da cewa an samu saukin matsalar Boko Haram, amma har yanzu akwai matsalar garkuwa da mutane cikinmu."

"Tsagerun sun fara da satan shanu, daga baya suka koma kashe-kahe, garkuwa da mutane, yiwa mata fyade, kona kauyuka da sace kayan abincin mutanen jihar."

Ya yi bayanin cewa rashin hadin kai tsakanin gwamnonin Arewa maso yamma ya bada gudunmuwa wajen tsanantan matsalar da ta addabi yankin.

DUBA NAN: Auwalu Daudawa: Abin da yasa na mika bindigu na 20 ga gwamnatin Zamfara

A bangare guda, gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Rotimi Akeredolu, ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir, kuma ya siffanta shi matsayin dan rikici da tarzoma.

Akeredolu wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin yankin kudu maso yamma ya yiwa Bala Kauran wankin babban bargo ne kan maganar da yayi cewa Fulani Makiyaya na da hakkin rike bindigu don kare kansu.

A farkon makon nan gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa Makiyaya na rike bindigogi ne domin kare kawunansu daga masu satar shanu, suna kwashe muku dukiya.

Source: Legit.ng

Online view pixel