Dan ta'adan ISIS ya kashe abokansa yan ta'adda 21 cikin kuskure yayin tafiya kai harin kunar bakin wake

Dan ta'adan ISIS ya kashe abokansa yan ta'adda 21 cikin kuskure yayin tafiya kai harin kunar bakin wake

Wani dan kunar bakin waken kungiyar ISIS a kasar Iraki ya hallaka abokansa akalla 21 inda ya tayar da bom cikin mota cikin kuskure, rahoton BBC.

Kwamandan Sojojin yankin Samarra a kasar Iraqi ya bayyana cewa sun tunanin dan kunar bakin waken ya danna wani oda a jikin motar ne da niyyan bankwana da abokansa mayakan ISIS.

Dan kunar bakin waken ya manta cewa an hada bam din da botirin odan motar.

Samarra wani birni ne a kasar Iraqi. Yana gabashin yankin Tigiris karkashin jagorancin Saladin, da nisan kilomita 125 da babbar birnin kasar, Bagdada.

Duk da yunkurin Sojojin Amurka da Iran, har yanzu yan ta'addan ISIS na cigaba da kai hareharen kunar bakin wake a kasar Iraqi.

Dan ta'adan ISIS ya yi kuskuren kashe abokan kunar bakin wakensa 21
Dan ta'adan ISIS ya yi kuskuren kashe abokan kunar bakin wakensa 21
Source: Getty Images

Source: Legit.ng

Online view pixel