Kwankwasiyya ta yi Alla-wadai da shirin rusa gadar saman da Ganduje ke kokarin yi

Kwankwasiyya ta yi Alla-wadai da shirin rusa gadar saman da Ganduje ke kokarin yi

- Mabiya tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso sun caccaki gwamna mai ci yanzu, Ganduje

- Wannan ba shi bane karo na farko da ake musayar kalamai tsakanin bangarorin biyu ba

- Wannan karon, Kwankwasiyya na zargin gwamnan da kokarin rusa ayyukan da Kwankwaso yayi a ofis

Mazhabar siyasa ta Kwankwansiyya ta nuna rashin amincewanta kan shirin da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ke yi na rusa daya daga cikin gadojin sama hudu da magabacinsa, Rabiu Musa Kwankwaso ya gina.

An ruwaito kwamishanan yada labaran jihar Kano, Muhammadu Garba, kwanakin baya da cewa gwamnatin na shirin rusa gasar Kofar Nasarawa kuma ta sake ginata domin saukakewa jama'ar Kano amfani da ita.

Amma mazhabar Kwankwasiya a jawabin da tsohon kwamishana lokacin mulkin Kwankwas Aminu AbdusSalam Gwarzo ya saki, ya siffanta wannan shiri na rusa gadar matsayin kokarin bita da kulli.

A cewarsa, an gina gadar Kofar Nasarawa ne ta yadda za'ayi shekara 100 ana cin moriyarta.

Kwankwasiyya ta lissafo jerin kayayyakin gwamnati da gwamna Ganduje ya rusa ko kuma take shirin sayarwa.

Wani sashen jawabin yace: "A ranar Talata, 9 ga Febrairu rahotanni sun jingina wani jawabi ga kwamishanan yada labaran Ganduje, Muhammad Garba inda yake fadawa Kanawa cewa gwamnan ya shirya rusa gadar Kofar Nasarawa."

"Abin takaici ne...gwamnan ya zabi rusa gine-gine da abubuwan tarihi da al'adan da Kano ke alfahari da su."

KU DUBA: Gwamnan jihar Bauchi ya bani kunya, Samuel Ortom na Benue ya caccaki Kaura

Kwankwasiyya ta yi Alla-wadai da shirin rusa gadar saman da Ganduje ke kokarin yi
Kwankwasiyya ta yi Alla-wadai da shirin rusa gadar saman da Ganduje ke kokarin yi
Source: Twitter

KU DUBA: Ana cece-kuce kan shugaban kwamitin Olympics na Qatar don ya ki musafaha da Alkalan wasa mata

Gabanin babban zaben da ke tafe a 2023, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya kamata a bawa kudancin Nigeria tikitin takarar kujerar shugaban kasa.

Ganduje ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today a Channels Television da aka haska a ranar Juma'a.

"Kudancin Nigeria ya dace a bawa takara amma ya kamata a samu hadin kai tsakaninsu," ya ce a yayin da ya ke amsa tambayar game da yankin da ya dace ta fitar da shugaban kasa a 2023.:

Source: Legit.ng

Online view pixel