Ana cece-kuce kan shugaban kwamitin Olympics na Qatar don ya ki musafaha da Alkalan wasa mata

Ana cece-kuce kan shugaban kwamitin Olympics na Qatar don ya ki musafaha da Alkalan wasa mata

- Sheikh Joaan bin Hamad Al Thani ne ya gabatar da lambar yabo da zakarun wasan karshe na FIFA Club World Cup

- Babban jami'in gwamnatin kasar na Qatar amma ya ki gaisawa da alkalan wasa mata da sukayi kokarin musafaha da shi

- A gaba duniya Sheikh Joaan ya yi banza da hannayen matan yayinda suka mika masa don msafaha

Sheikh Joaan bin Hamad Al Thani ya ki musafaha da Alkalan wasan kwallo mata lokacin wasan karshe na gasar kungiyar kwallon duniya da FIFA ta shirya, Daily Mail ta ruwaito.

Bayan nasarar da Bayern Munich ta samu kan Tigres UANL a wasan kwallon da akayi ranar Alhamis, 11 ga Febrairu, an gabatar da lambobin yabo ga zakakurai cikin yan wasa.

An tattaro cewa lokacin da Alkalan wasa mata Edina Alves Batista da Nueza Back sukayi kokarin musafaha da Sheikh Joaan, ya yi banza da su.

Wasu sun bayyana cewa addinin Musulunci ya haramtawa namiji taba mace wacce ba muharraminsa ko matar aurensa ba.

Sheikh Joaan bin Hamad Al Thani kani kani na ga shugaban kasar Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, kuma shine shugaban kwamitin gasar Olympic.

Kasar Qatar za ta shirya gasar kwallon duniya a shekarar 2022, kuma hakan ya maishe ta kasar Larabawa ta farko da zata shirya gasar a tarihi.

DUBA NAN: Kwankwasiyya ta yi Alla-wadai da shirin rusa gadar saman da Ganduje ke kokarin yi

Ana cece-kuce kan shugaban kwamitin Olympics na Qatar don ya ki musafaha da Alkalan wasa mata
Ana cece-kuce kan shugaban kwamitin Olympics na Qatar don ya ki musafaha da Alkalan wasa mata Photo: Bryn Lennon
Asali: Getty Images

DUBA NAN: Shahrarren Jagoran Fulani, Saleh Bayari, ya rigamu gidan gaskiya

A bangare guda, kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya shirya tsaf don komawa kungiyar kwallon kafa ta West Bromwich Albion a wata yarjejeniya ta takaitaccen lokaci.

Dan wasan kwallon kafan mai shekaru 28 a duniya ya bar kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr a watan Oktoban 2020.

Kamar yadda Daily Mail ta tabbatar, kungiyar ta nemi visa saboda dan kwallon kafa kuma ta saka ranar Laraba a matsayin ranar da za a yi mishi gwajin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel