2023: Ya kamata mulkin ƙasa ya koma kudancin Nigeria, in ji Ganduje

2023: Ya kamata mulkin ƙasa ya koma kudancin Nigeria, in ji Ganduje

- Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Kano ya ce yana goyon bayan a mika mulki ga kudancin Nigeria a 2023

- Gwamnan ya ce duk da cewa tsarin karba-karba baya cikin kudin tsarin mulki, tsari ne da ke taimakawa a ci zabe

- Ganduje ya kuma ce yana kyautata zaton APC za ta sake cin zaben mulkin kasar a 2023 domin cigaban da aka samu a tsaro da tattalin arziki a karkashin mulkin Buhari

Gabanin babban zaben da ke tafe a 2023, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya kamata a bawa kudancin Nigeria tikitin takarar kujerar shugaban kasa.

Ganduje ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today a Channels Television da aka haska a ranar Juma'a.

2023: Ya kamata mulkin ƙasa ya koma kudancin Nigeria, in ji Ganduje
2023: Ya kamata mulkin ƙasa ya koma kudancin Nigeria, in ji Ganduje. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

"Kudancin Nigeria ya dace a bawa takara amma ya kamata a samu hadin kai tsakaninsu," ya ce a yayin da ya ke amsa tambayar game da yankin da ya dace ta fitar da shugaban kasa a 2023.

"Karba-karba duk da cewa bata cikin kundin tsarin mulkin jamhuriyar tarayyar Nigeria tsari ne na cin zabe."

DUBA WANNAN: Bidiyon rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan

Da aka masa tambaya shin ko APC ta tabuka abin a zo a gani tun bayan lashe zabe da ta yi a 2015, ya amsa da cewa eh.

Ya ce jam'iyyar APC a karkashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ta inganta tsaro sannan tana gyara tattalin arzikin kasar.

Ganduje ya ce yana kyautata zaton jam'iyyar mai mulki za ta yi nasara a babban zaben 2023 da ke tafe ta cigaba da jagorancin kasar.

KU KARANTA: A fara duban sabon watan Rajab daga daren Juma'a, in ji Sarkin Musulmi

Amma ya ce akwai bukatar jam'iyyar ta yi shiri mai kyau tare da bincike kan hanyoyin da suka fi dacewa domin sake cin zabe a kasar.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Source: Legit.ng

Online view pixel