A fara duban sabon watan Rajab daga daren Juma'a, in ji Sarkin Musulmi
- Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar ya umurci mutane su fara neman jinjirin watan Rajab
- Sarkin Musulmin ya bada sanawar ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Wazirin Fadarsa, Farfesa Sambo Wali
- Sanarwar ta umurci al'umma su fara duban jinjirin watan da zarar rana ta fadi a yau Alhamis
Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Nigeria, NSCIA, ta ce al'ummar musulmi su fara duba sabon watan Rajab a kalandar musulunci daga Juma'ar gobe, Aminiya ta ruwaito.
Sanarwar ta NSCIA da sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ke jagoranta ta ce Juma'a ce zata kasance 29 ga watan Jumadal Akhira wanda zai yi dai-dai da 12 ga watan Fabrairun shekarar 2021.
DUBA WANNAN: Jiragen yakin NAF sun sake halaka yan bindiga masu yawa a Kaduna
Kazalika, sanarwar ta umurci al'umma da su kai rahoton ganin jaririn watan ga dagaci ko mai unguwa mafi kusa da su domin isar da sakon da ganin jaririn watan ga Sarkin Musulmi.
Sanarwar wacce Wazirin Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Professor Sambo Wali Junaidu ya saka wa hannu ta ce a fara duban jinjirin watan bayan faduwar rana.
KU KARANTA: Tsohon gwamnan Zamfara, Yerima, ya gurfana gaban kwamiti kan zargin 'azabtar da ɗan kasuwa'
Watan Rajab shine na takwas cikin jerin watannin da ke kalandar Musulunci ta Hijra, mai biye masa kuma shine watan Ramadan.
A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.
Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.
Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya tuntuɓarsa kai tsaye a shafinsa na Twitter @ameeynu
Asali: Legit.ng