Ahmed Musa ya shirya tsaf don komawa wata kungiyar kwallon kafa
- Shaharraren dan kwallon kafan Najeriya, Ahmed Musa ya shirya tsaf don komawa kungiyar West Bromwich
- Kyaftin din kungiyar Super Eagles din ya bar kungiyar Al Nassr da ke Saudi Arabia a watan Oktoban 2020
- An gano cewa sabuwar kungiyar da zai koma ta nema masa Visa kuma a ranar Laraba zai je gwajin lafiya
Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya shirya tsaf don komawa kungiyar kwallon kafa ta West Bromwich Albion a wata yarjejeniya ta takaitaccen lokaci.
Dan wasan kwallon kafan mai shekaru 28 a duniya ya bar kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr a watan Oktoban 2020.
DUBA WANNAN: Muna samun nasara a yaki da ta'addanci da 'yan bindigan daji, Sojin Najeriya
Kamar yadda Daily Mail ta tabbatar, kungiyar ta nemi visa saboda dan kwallon kafa kuma ta saka ranar Laraba a matsayin ranar da za a yi mishi gwajin lafiya.
Musa ya bar kungiyar CSKA da ke Moscow a 2016. Ya saka kwallo 55 a raga a wasanni 167 da yayi a Rasha inda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Leicester City a bazarar shekarar.
Abubuwa basu tafi ba kamar yadda aka so ba saboda ya samu nasara 7 a fitowa 21 da yayi.
Hakan yasa daga bisani ya koma CSKA a tsakanin 2017 zuwa 2018.
KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna ta bayyana ranar komawa makarantun gaba da sakandare na jihar
Daga nan ne ya koma kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr a watan Janairun 2019 kuma yayi wasa 62 kafin ya bar kungiyar.
A wani labari na daban, a ranar Alhamis rundunar sojin Najeriya tace tana samun nasarori, kuma tana dab da kawo karshen ta'addanci da rashin tsaro a kasar nan.
kakin rundunar soji, Manjo janar John Enenche ya sanar da hakan a wani taro a Abuja.kakin rundunar soji, Manjo janar John Enenche ya sanar da hakan a wani taro a Abuja.
Enenche ya bayar da misalin yadda suka ci karfin ta'addanci a jihar Zamfara da Katsina.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng