Shahrarren Jagoran Fulani, Saleh Bayari, ya rigamu gidan gaskiya

Shahrarren Jagoran Fulani, Saleh Bayari, ya rigamu gidan gaskiya

- Inna lillahi wa inna ilaihi Raji'una, Fulani a Najeriya sun yi rashin babban jigo

- An yi Jana'izarsa a da safiyar yau a garin Jos

Allah ya yiwa wani shahrarren jagoran Fulani makiyaya kuma dan jarida, Sale Bayari, rasuwa.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Bayari ya mutu ne da daren Alhamis a asibitin koyarwan jami'ar Jos, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Gabanin mutuwarsa, ya kasance shugaban uwar kungiyar Gan Allah Fulani na Najeriya GAFDAN, kuma tsohon Sakataren uwar kungiyar makiyayan Miyetti Allah (MACBAN),

Shugaban GAFDAN na jihar Plateau, Garba Abdullahi Muhammad, ya tabbatar da mutuwar Bayari.

An yi jana'izarsa da safiyar Juma'a bisa koyarwan addinin Musulunci.

KU KARANTA: Ana iya amfani da NIN don gano ɓata-garin makiyaya, in ji Ganduje

Shahrarren Jagoran Fulani, Saleh Bayari, ra rigamu gidan gaskiya
Shahrarren Jagoran Fulani, Saleh Bayari, ra rigamu gidan gaskiya Credit: dailytrust.com/prominent-fulani-leader-sale-bayari-is-dead
Source: UGC

KU KARANTA: Rashin tsaro: An maka Buhari da Makinde a kotu kan rikicin makiyaya a Oyo

A bangare guda, an yi jana'izar gwamnan farin hulan farko na jihar Legas, Alhaji Lateef Kayode Jakande, ranar Juma'a, 12 ga watan Febrairu, 2021.

Shahrarren dan siyasan kuma dan jaridan ya mutu ne ranar Alhamis yana mai shekaru 91.

An yi Sallar Jana'izar ne a gidansa dake Ilupeju na jihar Legas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel