Yanzu-yanzu: Ranar Juma'a za a yi jana'izar Alhaji Lateef Jakande

Yanzu-yanzu: Ranar Juma'a za a yi jana'izar Alhaji Lateef Jakande

- An bayyana ranar da za a birne gwamnan farar hula na farko a jihar Legas Alhaji Lateef Jakande

- Sanarwar da kwamitin abokansa suka fitar ta ce gobe Juma'a misalin karfe 4 za a birne marigayin

- Daya daga cikin yayansa mai suna Deji shima ya tabbatar da cewa gobe za a yi jana'izar mahaifinsa

Gobe Juma'a 11 ga watan Fabrairun 2021 ne za a yi jana'izar dattijon kasa kuma gwamnan farar hula na farko a jihar Legas, Alhaji Lateef Jakande, The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta fito ne daga bakin kwamitin abokan tsohon gwamnan ya da riga mu gidan gaskiya a yau Alhamis.

Kazalika, daya daga cikin yayansa, Deji, ya tabbatar cewa za a yi jana'izar mahaifinsa a ranar Juma'a misalin karfe 4 na yamma.

DUBA WANNAN: Jiragen yakin NAF sun sake halaka yan bindiga masu yawa a Kaduna

Yanzu-yanzu: Ranar Juma'a za a yi jana'izar Alhaji Lateef Jakande
Yanzu-yanzu: Ranar Juma'a za a yi jana'izar Alhaji Lateef Jakande. Hoto: @MobilePunch
Source: Facebook

A cikin sanarwar da wakili majiyar Legit.ng ya samu, abokan Jakande sun ce za a yi addu'o'i na musamman a gidan marigayin da ke Ilupeju a Legas kafin a birne shi.

Sanarwar na dauke da sa hannun tsohon shugaban jami'ar jihar Legas Farfesa Abisogun Leigh, Kamal Giwa, Prince Bayo Oshiyemi, Alhaji Gani Owolabi Dada, Mrs. Omolara Abeke Vaugh, da Alhaja Latifat Gbajabiamila.

KU KARANTA: Tsohon gwamnan Zamfara, Yerima, ya gurfana gaban kwamiti kan zargin 'azabtar da ɗan kasuwa'

Sanarwar ta ce, "Kwamitin abokan LKJ gwamnan farar hula na farko a jihar Legas na sanar da rasuwar shugaban mu Baba Kekere na Legas, Alhaji Chief Lateef Kayode Jakande, da ya rasu yau Alhamis 11 ga watanFabrairun 2021 yana da shekaru 91 a duniya.

"Ga tsarin yadda za a yi jana'izarsa kamar haka - Za a yi addu'o'i a gida mai lamba 2 Bishop Street Illupeju, jihar Legas a ranar Juma'a 12 ga watan Fabrairun 2021 misalin karfe 9 na safe.

"Za a birne shi a Volts and Gardens Ikoyi misalin karfe 4 na yamma a ranar Juma'a 12 ga watan Fabrairun 2021."

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya tuntuɓarsa kai tsaye a shafinsa na Twitter @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel