CNG ta goyi bayan Sheikh Gumi na neman gwamnati ta yi wa yan bindiga afuwa

CNG ta goyi bayan Sheikh Gumi na neman gwamnati ta yi wa yan bindiga afuwa

- Gamayyar kungiyoyin arewa, CNG, ta nuna goyon bayanta ga neman afuwa da Sheikh Gumi ke son ganin an yi wa yan bindiga

- Kungiyar ta kuma soki gwamnonin arewa kan matakin haramta kiwo a fili ba tare da tanadin tsarin taimakawa makiyaya ba

- Har wa yau, kungiyar ta soki gwamnatin tarayya a kan abinda ta kira gazawarta wurin daukan matakan kawo karshen rikicin

Gamayyar kungiyoyin arewa, CNG, ta goyi bayan Sheikh Ahmed Gumi na kira ga gwamnati ta yi wa yan bindigan da ke adabar jihohin arewa afuwa da nufin samun dawamammen zaman lafiya a yankin, Leadership ta ruwaito.

Kakakin CNG Abdul Azeez Suleiman cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a Abuja, ya yi kira ga makiyaya Fulani da ke zaune a jihohin kudu su dawo idan har garuruwan da suke ba su maraba da su.

Gamayyar kungiyoyin arewa ta goyi bayan yi wa yan bindiga afuwa
Gamayyar kungiyoyin arewa ta goyi bayan yi wa yan bindiga afuwa. @LeadershipNGA
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Damfarar N500,000: An yanke wa ma'aikacin gwamnatin Kano shekaru 5 a gidan ɗan kande

Ya ce, "Ba mu goyon bayan matakin da kungiyar gwamnonin arewa ta dauka na haramta kiwo a fili ba tare da kirkirar filayen kiwo ba bayan shafe shekaru hudu suna karyar za su bawa makiyayan matsuguni ta hanyar wasu shirye-shirye da har yau suka gaza yi.

"Muna ankarar da mutane kan yadda gwamnatin tarayya ta gaza daukan wani matakin na gaske don kawo karshen matsalar da hadin kan Nigeria.

"Muna goyon bayan Sheikh Ahmed Gumi a shirinsa na ganawa da yan bindiga da nufin ganin an musu afuwa, sauya tunani da cigaba da zama cikin mutane da wadanda suka rungumi zaman lafiya sannan a ragargaji wadanda ba su amince ba.

KU KARANTA: Jiragen yakin NAF sun sake halaka yan bindiga masu yawa a Kaduna

"Don haka, muna goyon bayan kokarin da gwamnatocin Zamfara, Katsina, Sokoto, Kebbi da wasu jihohi ke yi na sulhu a maimakon tsarin amfani da karfin bindiga da zubar da jini da irin na El-Rufai da masu ra'ayinsa," in ji shi.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya tuntuɓarsa kai tsaye a shafinsa na Twitter @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel