Damfarar N500,000: An yanke wa ma'aikacin gwamnatin Kano shekaru 5 a gidan ɗan kande

Damfarar N500,000: An yanke wa ma'aikacin gwamnatin Kano shekaru 5 a gidan ɗan kande

- Alkali ya yanke wa wani ma'aikacin gwamnatin jihar Kano hukuncin shekaru 5 a gidan gyaran hali

- Hukumar ICPC ta yi karar wanda aka yanke wa hukuncin, Mohammed Hassan, a kotu kan zarginsa da damfarar gwamnatin jihar kudi N513,445

- Da farko ya musanta zargin amma daga bisani ya nemi a yi sulhu inda ya ce zai mayar wa gwamnati da kudin da ya zare daga asusunta

Babban kotu a jihar Kano ta yanke wa wani Mohammed Ibrahim Hassan, ma'aikacin hukumar tsara birane da cigaba, KNUPDA, hukuncin zaman gidan yari na shekaru 5 saboda damfarar gwamnati kudi N513,445, LIB ta ruwaito.

Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ce ta gurfanar da Hassan kan tuhumansa da laifuka hudu da suka hada da kirkirar rasit din asusun gwamnatin jihar Kano da niyyar karyar cewar ya mayarwa gwamnatin jihar kudin.

An yanke wa ma'aikacin gwamnati a Kano hukuncin shekaru 5 a gidan ɗan kande
An yanke wa ma'aikacin gwamnati a Kano hukuncin shekaru 5 a gidan ɗan kande. Hoto: @thecableng
Source: Twitter

Masu shigar da karar sun shaidawa kotun cewa laifin ta sabawa sashi na 25(1)(a) na dokar rashawa da laifuka masu alaka da rashawar ta 2000 da wasu sassan na dokar Penal Code na jihar Kano.

DUBA WANNAN: An nada Mohammed Yerima a matsayin sabon kakakin sojojin Nigeria

Takardar karar ta nuna cewa Hassan ya aikata laifin tsakanin watan Yunin 2017 da Maris din 2018 inda ya kirkiri rasit din asusun gwamnatin na jihar Kano domin yin karyar cewa ya mayar da N299,509 da N213,935 a lokuta daban daban amma bai mayar ba.

Ya musanta laifukan da aka karanto masa amma daga baya ya sauya ya nemi su sasanta da gwamnatin inda ya amince zai biya N513,445.

KU KARANTA: Saki: Mata ta mayarwa miji sadakin N28,000 da ya biya yayin aurenta shekaru 7 da suka shude

Alkalin, Mai shari'a Lawal Wada ya yanke masa hukuncin shekaru biyar a gidan yari ko kuma ya biya tarar N100,000. Ya kuma yanke hukuncin cewa wanda akayi karar zai biya gwamnatin Kano N513,445.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel