Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Legas na farko, Alhaji Lateef Jakande, ya mutu

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Legas na farko, Alhaji Lateef Jakande, ya mutu

Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa tsohon gwamnan jihar Legas, Alhaji Lateef Jakande, ya rigamu gidan gaskiya.

An ce Alhaji Jakande ya rasu ne yana da shekaru 91.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da hakan a shafinsa na Tuwita ranar Alhamis.

"Ina mai sanar da mutuwar mutumin kirki, babban dan siyasa, kuma gwamnan jihar Legas na farko, Alhaji Lateef Kayode Jakande," Sanwo Olu yace.

Tsohon gwamnan, wanda aka fi sani da Baba Kekere, ya yi ayyukan cigaba da dama lokacin da mulki jihar tsakanin Oktoba 1979 da Disamba 1983.

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Legas na farko, Alhaji Lateef Jakande, ya mutu
Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Legas na farko, Alhaji Lateef Jakande, ya mutu
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng