Jihohi 10 da masu kudi suka fi sanya hannun jari shekarar 2020, 5 na Arewa
Wani rahoton The Cable ya nuna cewa har yanzu jihar Legas ce jiha mafi janyo hankalin masu arziki wajen sanya hannun jari cikin jihohin Najeriya 36.
Hannun jarin da jihar Legas kadai ke samu ya fi na sauran jihohin Najeriya gaba daya idan aka hada su.
Legit.ng ta lura cewa rahoton wacce aka nakalto daga Cibiyar Lissafin Najeriya ya nuna cewa Legas ta samu $8.31 billion na hannun jari.
Ga jerin jihohin nan:
1. Lagos - $8.31 billion
2. Abuja (FCT) - $1.27 billion
3. Abia - $56.07 million
4. Niger - $16.36 million
5. Ogun - $13.39 million)
6. Anambra - $10.02 million
7. Kaduna - $4.03 million
8. Sokoto - $2.50 million
9. Kano - $2.38 million
10. Akwa Ibom - $1.05 million
KU KARANTA: Filayen jirgin saman Najeriya suna daga cikin masu muni a duniya, in ji wata hukuma
KU DUBA: Makiyaya 4,000 sun yi hijra daga jihohin kudu zuwa jihar Kaduna
A bangare guda, majalisar Dattawa a ranar Laraba ta tabbatar da nadin Ahmed Kuru da Bello Hassan a matsayin shugabannin Hukumar Kula da Kadarori ta Kasa da Hukumar Inshora, AMCON, da Hukumar NDIC kasa kamar yadda aka jero su.
Tabbatarwa na zuwa ne bayan nazarin kan rahotannin kwamitin majalisa kan bankuna da inshora da wasu hukumomin hada-hadar kudade.
Kazalika, an tabbatar da Ebelechukwu Uneze a matsayin shugaban AMCON da Muhammad Ibrahim a matsayin shugaban hukumar Nigeria ta Inshora.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng