Hukumar Kwastam ta damke tankar mai cike da buhuhunan shinkafa 'yar waje

Hukumar Kwastam ta damke tankar mai cike da buhuhunan shinkafa 'yar waje

- Jami'an hukumar Kwastam sun yi babban kamu a jihar Katsina

- Har yanzu gwamnatin tarayya ta haramta shigo da shinkafa daga kasashen waje

- Gwamnatin Buhari ta yi hakan ne domin karfafa manoman shinkafa a Najeriya

Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar hana fasa kwabri a Najeriya (NCS) shiyar jihar Katsina ta damke tankar man fetur da ake amfani wajen shigo da shinkafa yar waje zuwa Najeriya.

Ariya Kontrolan Kwastam na jihar, Adewale Musa Aremu, yayin bayyana kayayyakin da aka damke ya bayyana cewa masu fasa kwabrin sun boye manyan buhuhunan shinkafa 50kg guda 210 cikin tankar.

Ya ce an kwace motar ne a Dutsinma bayan jami'an sun samu rahoton cewa tankar man na dauke da shinkafa maimakon man fetur.

Motar mai lamba SBG 419 XA na dauke da fostan kamfanin A.A Rano wanda ake tunanin na boge ne.

Kontrola Aremu ya ce an damke mutanen da ke cikin motar da kuma wani mutumi wanda ya je hedkwatar hukumar da sunan cewa tankarsa ce.

A cewarsa, ana gudanar da bincike kafin daukan mataki kan su.

DUBA NAN: Femi Fani-Kayode ya sauya sheka jam'iyyar APC, Yahaya Bello

Hukumar Kwastam ta damke tankar mai cike da buhuhunan shinkafa 'yar waje
Hukumar Kwastam ta damke tankar mai cike da buhuhunan shinkafa 'yar waje
Asali: UGC

KU KARANTA: Hukumar Kwastam ta damke tankar mai cike da buhuhunan shinkafa 'yar waje

Bugu da kari, hukumar ta damke motocin da ake kokarin shigo da su Najeriya ta barauniyar hanyar guda hudu.

Daga ciki akwai mota kirar BMW 2014, Toyota Hilux 2020 da Toyota Land Cruiser, da kuma babbar mota dauke da buhuhunan shinkafa.

Aremu ya yi gargadin cewa jami'anta dake jihar Katsina ba zasuyi kasa a gwiwa wajen gano sabbin dabarun da ake amfani da su wajen fasa kwabri ba.

A wani labarin kuwa, Mista Umar Ndashacba, Manajan Shirye-shirye na Shirin Ciyar da Makarantun Gida na Kasa (NHGSFP) a Neja, ya ce aƙalla an samar da ayyuka sama da 14,000 a cikin shekaru biyu da kasancewar shirin a jihar.

Ndashacba ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

"Duk da cewa an kaddamar da shirin a jihar a shekarar 2018, ta samar da ayyuka sama da 14,000 ga mata da kuma baiwa manoma damar bunkasa noman."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng