Da a gina Masallatai ko Islamiyyu, gwara a zuba kudi a harkar Fim, Aliyu Momoh

Da a gina Masallatai ko Islamiyyu, gwara a zuba kudi a harkar Fim, Aliyu Momoh

- Jama'a a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun tofa albarkatun bakinsu kan maganar shahrarren dan wasan kwaikwayo, Ali Momo

- Momo babban jarimi ne wanda ya dade a masana'antar Kannywood

- Dan wasan kwaikwayon ya bayyana muhimmancin shirya fina-finan Hausa

Aliyu Momoh ya bayyana ra'ayinsa kan muhimmancin harkar Fim a cikin al'umma inda yayi kira da zuba kudi cikin masana'antar Kannywood.

A ra'ayinsa, da a zuba kudi wajen gina Masallatai ko Islamiyyu a kasar Hausa, gwara a zuba kudin wajen harkar shirya fina-finan Hausa.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa fitaccen Jarumi a masana'anatar Kannywood ya bayyana wannan kalaman a cikin shirn ‘Barka da hantsi’ na rediyo freedom dake Kano a safiyar yau Laraba.

Yace: "A halin da ake ciki yanzu da a gina Masallatai da Islamiyyu gara a zuba kudaden a harkar shirya fina-finan Hausa."

KU KARANTA: Hukumar Kwastam ta damke tankar mai cike da buhuhunan shinkafa 'yar waje

Da a gina Masallatai ko Islamiyyu, gwara a zuba kudi a harkar Fim, Aliyu Momoh
Da a gina Masallatai ko Islamiyyu, gwara a zuba kudi a harkar Fim, Aliyu Momoh Hoto: Aminiya
Source: Twitter

KU DUBA: Femi Fani-Kayode ya sauya sheka jam'iyyar APC, Yahaya Bello

A wani labarin kuwa, manyan jarumai mata na Kannywood na can a kasar Dubai suna yawon bude ido da shakatawa. Wannan ya zama kamar al’ada ga wasu yan masana’antar inda suke tafiya chan a duk karshen shekara domin hutawa.

Daga cikin manyan jaruman masana’antar da ke can Dubai akwai Fati Washa, Hafsat Idris, Hadiza Gabon, Rahama Sadau, Nafisat Abdullahi da kuma Maryam Wazeeri.

Jaruman dai kan dora hotunansu a shafukansu na sada zumunta kan tafiyar tasu tare da fadin ‘On Dubai’. Read more:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel