Zulum ko tawagarsa ba suyi hadarin mota ba, Mai magana da yawunsa yayi martani

Zulum ko tawagarsa ba suyi hadarin mota ba, Mai magana da yawunsa yayi martani

- Gwamnan Borno ya bayyana ainihin abinda ya faru ranar Laraba

- Gwamnan, mukarrabansa da manya yan siyasa sun raka shi karamar hukumarsa don sabunta rijistar zama dan APC

- Daya daga cikin wadanda suka rakashi ya samu hadarin mota kuma ya mutu

Tawagar gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, bata yi hadari ba, mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, ya yi fashin baki.

Isa Gusau ya yi wannan bayani ne don martani kan rahoton da wasu jaridu sukayi na cewa motar gwamna Zulum ta yi hadari.

A cewar Gusau, Zulum yana Mafa lokacin da hadarin ya auku kuma ko hanya bai shiga ba lokacin.

Amma ya tabbatar da cewa lallai hadari ya auku a hanyar kuma shugaban Kanuri na jihar Legas ya mutu sakamako.

Jawabin yace: "Muna son yin fashin bakin cewa tawagar motocin gwamna Babagana Umara Zulum, bata samu wani hadari kamar yadda ake radawa ba. Rahoton karya ne."

Mai magana da yawun gwamnan ya ce Mai Kanuribe na Legas, Alhaji Mustapha Muhammad, ne ya samu hadari kuma su uku suka rasa rayukansu a hanyar yayin komawa Maiduguri bayan takawa gwamnan baya zuwa Mafa.

"Ko shakka babu Mai (Kanuribe na Legas) ya je Mafa domin takawa gwamna Zulum baya. Amma lokacin da Mai ya shiga hanyar komawa Maiduguri, gwamnan na Mafa," Gusau yace

"Gwamnan tare da Sanata Kashim Shettima da wasu shugabanni sun ga hadarin a hanya kuma suka raka gawawwakin Mai da sauran zuwa iyalansu a Maiduguri domin jana'iza."

KU DUBA: Da a gina Masallatai ko Islamiyyu, gwara a zuba kudi a harkar Fim, Aliyu Momoh

Zulum ko tawagarsa ba suyi hadarin mota ba, Mai magana da yawunsa yayi martani
Zulum ko tawagarsa ba suyi hadarin mota ba, Mai magana da yawunsa yayi martani Credit: The Governor of Borno State
Source: Facebook

KU KARANTA: Hukumar Kwastam ta damke tankar mai cike da buhuhunan shinkafa 'yar waje

A bangare guda, wakilan Najeriya sun isa Marwa, a Kamaru domin dawo da ‘yan gudun hijirar Najeriya 9,800.

'Yan gudun hijra 9,800 sune wadanda ke cikin matakin farko na dawo da su daga Kamaru daga cikin ‘yan Najeriya 46,000 da ke samun mafaka a sansanin Minawao da ke kasar Afirka ta Tsakiya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Borno, Malam Isa Gusau, ya fitar a ranar Laraba, ta ce maigidan nasa ya isa Marwa ne tare da jami’an ma’aikatar kula da ayyukan jin kai ta tarayya,da ci gaban jama’a don dawo da ‘yan Nijeriya 9,800 kasarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel