Yan sanda sun dakile harin masu garkuwa da mutane a Zamfara, sun kwace babura da makamai

Yan sanda sun dakile harin masu garkuwa da mutane a Zamfara, sun kwace babura da makamai

- Jami'an tsaro sun samu galaba kan yan bindiga a wani artabu a Zamfara

- Kwamishanan tsaron jihar tare da kwamishanan yan sanda sun yi hira da manema labarai

- Wannan ya biyo bayan mika wuyan Auwalu Daudawa, wanda ya jagoranci sace yaran Makarantan Kankara

Jami'an hukumar yan sandan Najeriya sun samu nasaran dakile wani mumunan harin da yan bindiga da fashi da makami suka kai jihar Zamfara.

Kwamishanan yan sandan jihar, Yaro Abutu, a ranar Talata ya bayyana irin makamai da kayyayakin Sojojin da aka kwato daga wajen yan bindiga.

A cewarsa, yan bindiga sun gudu sun bar baburansu akalla 14 yayinda yan sanda suka bude musu wuta.

Hakazalika an gano kayan Sojojin jamhuriyyar Nijar a wajen yan bindigan wanda suke amfani da shi wajen badda kama.

Yaro ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Gusau, babbar birnin jihar Zamfara, TVC News ta ruwaito.

"Mun kwato wadanda baburan ne daga wajen tsagerun yan bindiga, wanda suka gudu yayinda yan sanda suka kure musu gudu. Da yawa cikinsu sun jigata," ya bayyana.

"Bayan haka, mun gano kayan Sojoji dauke da tambarin hukumar Sojin jamhuriyyar Nijar."

Shi kuwa kwamishanan tsaron jihar Zamfara, Abubakar Dauran, ya jaddada muhimmacin sulhu da yan bindigan domin tabbatar da zaman lafiya cikin al'umma.

Saboda haka, ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewa maso yamma musamman Kastina, Kebbi, Sokoto, Neja da Kaduna su bi sahun jihar Zamfara don kawo karshen matsalar tsaro.

Yan sanda sun dakile harin masu garkuwa da mutane a Zamfara, sun kwace babura da makamai
Yan sanda sun dakile harin masu garkuwa da mutane a Zamfara, sun kwace babura da makamai Hoto: @TVCNewsng
Source: Twitter

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin ginin layin dogon Kano-Jigawa-Katsina-Maradi

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta kashe N37bn a tallafin 'Survival Fund', in ji Osinbajo

A wani labarin kuwa, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mataimaki na musamman ga Mataimakin Gwamnan Taraba, Alhaji Bala Baba.

Wata majiya daga danginsa ta shaida wa jaridar The Nation cewa an sace Bala ne a gidansa da ke yankin Sabongari na Jalingo da misalin karfe 1.30 na safiyar ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu.

A cewar majiyar, 'yan bindigar sun mamaye yankin, inda suka yi ta harbi ba kakkauta na sama da mintuna 30 kafin suka tafi da shi.

Source: Legit.ng

Online view pixel