Sabbin mutane 1,624 sun kamu da Korona a Najeriya ranar Juma'a, an sallami 1,190

Sabbin mutane 1,624 sun kamu da Korona a Najeriya ranar Juma'a, an sallami 1,190

- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara

- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake kafa dokar hana fita idan adadin ya cigaba da karuwa

- Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan dokar hukunta masu saba dokokin da NCDC ta kafa

A ranar Juma'a, 05 ga watan Febrairu 2021, Mutane 1,624 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.

Hakazalika an sallami mutane 1,190 a ranar.

Daga cikin wadanda aka sallama, akwai mutane 831 da sukayi jinya cikin gidajensu a Legas, 85 a Kaduna.

Abin takaici, mutane 9 sun rasa rayukansu.

Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 137,654 a Najeriya.

Daga cikin mutanen da suka kamu, an sallami 111,639 yayinda 1,641 suka rigamu gidan gaskiya.

KU KARANTA: Dan jaridar VOA Hausa, Ibrahim AbdulAziz ya rigamu gidan gaskiya

DUBA NAN: World Bank ta baiwa Najeriya gudunmuwan $500m don inganta wutan lantarki

A bangare guda, shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan sabon dokan daurin watanni 6 a gidan kaso kan duk wanda aka kama yana saba dokokin kariya daga cutar Korona.

Shugaban kasan ya rattafa hannunsa dokar a Abuja, ranar Laraba.

Kamar yadda dokar killata, sashe 34 na sabon dokan ya tanada, duk wanda ya saba, za'a ci shi tara ko kuma yayi watanni shida a Kurkuku.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel