World Bank ta baiwa Najeriya gudunmuwan $500m don inganta wutan lantarki

World Bank ta baiwa Najeriya gudunmuwan $500m don inganta wutan lantarki

- Bankin Duniya ta baiwa Najeriya wani tallafi mai muhimmanci ga al'umma

- Najeriya na cikin kasashe mafi fama da rashin wutan lantarki a duniya, cewar bankin duniya

- Kusan rabin yan Najeriya basu gani hasken wutan lantarki gaba daya

Bankin duniya (World Bank) ta taimakawa Najeriya da kudi $500m don inganta wutan lantarki da kuma karfafa kamfanonin raba wutan lantarki a kasar.

A jawabin da bankin ta saki ranar Juma'a, za ta baiwa kamfanonin dake raba lantarki da sharadin sun cimma manufar inganta wutan lantarki da mutane.

Jawabin yace, "Yan Najeriya milyan 85 ba su da wutan lantarki. Hakan na nufin cewa kashi 43% na jama'ar kasar kuma Najeriya ce kasar dake gaba wajen rashin isasshen wutan lantarki."

"Rashin lantarki babban kalubalee ne ga al'umma da kasuwancinsu, kuma hakan na sabbasa hasarar kimanin $26.2 billion (₦10.1 trillion)."

"Bisa rahoton saukin kasuwanci da World Banka ta saki a 2020, Najeriya ce kasa ta 171 cikin kasashe 190 da ake ganin rashin lantarki ne babban kalubale ga kamfanonin masu zaman kansu."

Jawabin ya nakalto Diraktan World Bank na Najeriya, Shubham Chaudhuri da cewa, "Inganta wutan lantarki na da muhimmanci wajen rage talauci da inganta tattalin arziki bayan annobar COVID-19."

Hadimin Buhari, Tolu Ogunlesi, ya tabbatar da wannan labari a jawabin da yayi a shafinsa na Tuwita.

KU KARANTA: Nan da 2025, kashi 30 na motocin Najeriya da lantarki zasu rika amfani, Jelani Aliyu

World Bank ta baiwa Najeriya gudunmuwan $500m don inganta wutan lantarki
World Bank ta baiwa Najeriya gudunmuwan $500m don inganta wutan lantarki
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Buhari zai kaddamar da ginin layin dogon Kano-Maradi, Kano-Dutse

A bangare guda, gwamnatin tarayyar Najeriya na harin tabbatar da cewa nan da shekaru hudu masu zuwa, kashi 30 na motocin da za'a rika amfani da su a Najeriya su kasance masu amfani da wutan lantarki.

A jawabin da yayi kaddamar da motar lantarki ta farko da aka hada a Najeriya, shugaban hukumar zane da cigaba motoci a Najeriya, Jelani Aliyu, ya bayyana cewa lokacin amfani da mota mai lantarki a Najeriya yayi.

Aliyu ya ce ba za'a bar Najeriya a baya ba yayinda duniya ke cigaba wajen daina amfani da motoci masu amfani da man fetur, Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng