Yanzu-yanzu: Dan jaridar VOA Hausa, Ibrahim AbdulAziz ya rigamu gidan gaskiya

Yanzu-yanzu: Dan jaridar VOA Hausa, Ibrahim AbdulAziz ya rigamu gidan gaskiya

Wani dan jaridar Muryar Amurka (VOA Hausa) dake dauko rahoto daga jihar Adamawa da Taraba, Ibrahim Abdulaziz ya mutu mumunan hadarin motar da ya auku a hanyar Gombe-Alkaleri.

Dan jaridar wanda yayi shekara 48 a duniya ya yi aiki da gidajen jaridu da yawa kuma ya yi shirye-shirye a gidajen rediyo irinsu Radio Gotel da FRCN Fombina FM Yola.

Iyalan mamacin sun tabbatar da labarin mutuwarsa, inda suka ce su biyu suka mutu a hadari.

Ya rasu yana da mata uku da yara tara.

Sakataren kungiyar yan jaridan Najeriya, shiyar jihar Adamawa, Fidelis Jocthan; ya yi alhinin rasuwar Ibrahim kuma ya yi addu'an Allah ya jikansa.

Yanzu-yanzu: Dan jaridar VOA Hausa, Ibrahim AbdulAziz ya rigamu gidan gaskiya
Yanzu-yanzu: Dan jaridar VOA Hausa, Ibrahim AbdulAziz ya rigamu gidan gaskiya
Asali: Original

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel