Gwamnatin Kano ta kai Sheikh AbdulJabbar Kotu, ta samu izinin kulle Masallacinsa da hanashi wa'azi
Gwamnatin jihar Kano ta samu izinin kotu domin kulle Masallacin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da kuma hanashi cigaba da wa'azi a fadin jihar.
Gwamnatin ta samu takardar izinin ne daga Alkali Mohammed Jibrin na kotun Majistare dake Gidan Murtala bayan karar da ofishin kwamishanan Shari'ar jihar ta shigar, rahoton Daily Trust.
Kotun ta bada umurnin garkame Masallacin da cibiyar Musulunci dake Filin Mushe, har sai an kammala binciken da hukumar yan sanda da wasu hukumomin tsaro ke yi.
Hakazalika, kotu ta umurci AbdulJabbar ya daina duk wani irin wa'azi da kalaman da ake ganin zai iya haddasa rikici ko rigima.
Hakazalika kotun ta umurci gidajen talabijin, rediyo, da kafafen yada labarai su daina sanya karatunsa har sai an kammala binciken.
Kotun ta umurci dukkan jami'an tsaro su tabbatar da cewa an bi wannan umurni.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng