Da duminsa: Oyetola ya umurci dukkan shugabannin ƙananan hukumomi su bar ofisoshinsu

Da duminsa: Oyetola ya umurci dukkan shugabannin ƙananan hukumomi su bar ofisoshinsu

- Gwamna Adegboyega Oyetola na jihar Osun ya umurci masu rike da mukaman siyasa a kananan hukumomin jihar su ajiye ayyukansu

- An bada wannan sanarwar ne sakamakon cikar wa'adin aikin shugabannin kananan hukumomin da ke jihar

- Mista Oyetola ya yi musu godiya bisa gudunmawar da suka bada wurin cigaban jihar tare da musu fatan alheri

Gwamnan jihar Osun, Mista Adegboyega Oyetola ya umurci dukkan shugabannin kananan hukumomi da sauran masu rike da mukaman siyasa a kananan hukumomin jihar su ajiye aikinsu.

Ya sanar da hakan ne cikin wata sanarwar da ya fitar ta bakin sakataren gwamnatin jihar, Prince Wole Oyebamiji mai taken 'sanarwa mai muhimmanci' a ranar Juma'a, The Punch ta ruwaito.

Yanzu yanzu: Gwamna Oyetola ya umurci dukkan shugabanin LG su ajye ayyukansu
Yanzu yanzu: Gwamna Oyetola ya umurci dukkan shugabanin LG su ajye ayyukansu. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamna Bala Mohammed: Yadda na kusa rasa aiki na saboda Jami'ar Baze

A cewar gwamnan, an bukaci masu rike da mukamman siyasar su ajiye ayyukansu ne saboda wa'adin aikinsu ya kare.

Sanarwar ta ce, "Mai girma gwamnan jihar Osun, Mista Adegboyega Oyetola ya umurci dukkan masu rike da mukaman siyasa a kananan hukumomi su fice daga ofisoshinsu su mika mulki ga ma'aikata mafi girma a kananan hukumominsu.

"Hakan na zuwa ne saboda cikar wa'adin ayyukan dukkan masu rike da mukaman siyasa a dukkan kananan hukumomi da masu rike da mukaman a Osun a ranar Juma'a, 5 ga watan Fabrairun 2021.

KU KARANTA: CNG: An sako jagororin Gamayyar Kungiyoyin Arewa da aka kama a Kaduna

"Gwamna Oyetola ya musu godiya bisa gudunmawar da suka bada wurin cigaban jihar kuma ya musu fatan alheri a duk wani abin da za su yi a gaba."

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel