CNG: An sako jagororin Gamayyar Kungiyoyin Arewa da aka kama a Kaduna

CNG: An sako jagororin Gamayyar Kungiyoyin Arewa da aka kama a Kaduna

- Jami'an tsaro sun sako Nastura Ashir Shariff da Balarabe Rufai da aka kama a Kaduna

- Jami'an hukumar DSS ne suka tafi da shugabannin biyu da safe bayan an hana su yin taro

- Kakakin CNG, ya ce ya yi magana da shugabannin sun kuma tabbatar masa suna cikin koshin lafiya

Gamayyar Kungiyoyin Arewa, CNG, a daren ranar Alhamis ta ce ta yi magana da shugabannin ta biyu: Nastura Ashir Shariff da Balarabe Rufai, da aka yi awon gaba da su da safe a Kaduna.

Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman, cikin sanarwar da ya aike wa Daily Trust ya ce, "Na yi magana da shugaban mu na kasa Balarabe Rufai ya tabbatar min an sake su da halin da suke ciki.

"Misalin karfe 10.30 na dare, Mista Rufai ya kira ya ce an dawo musu da wayoyin salularsu kuma an sake su sannan zai mini cikaken bayanin abinda ya faru da su daga bisani.

Da duminsa: An sako jagororin Gamayyar Kungiyoyin Arewa da aka kama a Kaduna
Da duminsa: An sako jagororin Gamayyar Kungiyoyin Arewa da aka kama a Kaduna. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano ta hana Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wa'azi a jihar

"Shariff kuma ya yi magana da ni ta wayar Rufai ya tabbatar min dukkansu suna cikin koshin lafiya."

Yadda aka kama su

Tunda farko, Suleiman ya ce jami'an hukumar yan sandan farar hula, DSS, ne suka kama su bayan direktan hukumar a jihar ya gargadi CNG kan taron da suka shirya yi a NAF Club Kaduna.

Kakakin na CNG ya ci gaba da bayani, "Bayan yan mintoci daga baya, sai aka kira mu daga NAF Club aka sanar da su cewa an umurce su daga sama da su hana mu amfani da dakin taron."

Kakakin ya ce sun je sun shaida wa manema labarai wadanda tuni suka hallara a wurin game da ci gaban inda ya nemi su watse saboda an dakatar da yin taron.

Sanarwar ta yi ishara da cewa, "A lokacin da muke barin NAF Club din kuma muna kan hanya a kusa da layin Nagogo sai wata mota kirar Peugeot a rufe ta rufe motar gabar wacce ke dauke da jami'an biyu kuma ta umarce su da su shiga Peugeot din kuma su yi sauri."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel