Munafikai ne kawai; Sule Lamido ya caccaki gwamnonin APC da ke zawarcin Jonathan

Munafikai ne kawai; Sule Lamido ya caccaki gwamnonin APC da ke zawarcin Jonathan

- Har yanzu rade-radin cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, zai koma APC basu daina yawo ba a kafafen yada labarai ba

- Wasu rahotanni sun bayyana cewa gwamnonin APC na son jawo Jonathan zuwa jam'iyyar domin yin takarar shugaban kasa a 2023

- Tsohon gwamna kuma jigo a jam'iyyar APC, Sule Lamido, ya caccaki gwamnonin APC akan rade-radin zawarcin Jonathan

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam'iyyar PDP, Sule Lamido, ya bayyana cewa gwamnonin Jam'iyyar APC da ke zawarcin Goodluck Jonathan domin ya gaji shugaba Buhari a 2023 munafikai ne.

A baya bayan nan, an hango gwamnonin jam'iyyar APC a ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala, na ƙus-ƙus da Jonathan a wata ganawar sirri a Abuja, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Jonathan, wanda ya sha kaye a zaɓen shugaban a 2015, har yanzu ya na da damar tsayawa takarar shugabancin ƙasa na wa’adi ɗaya na shekaru hudu a kan mulki.

KARANTA: An gano wata rigar sarauta da aka rina tun lokacin Annabi Dauda, shekaru 3000 baya

Da yake magana a gidan Talabijin na Arise ranar Laraba, Lamido ya yi mamakin dalilin da ya sa gwamnonin ke tunanin gabatar da Jonathan wanda suka bayyana a matsayin "mai rauni kuma wanda bai cancanta ba". Ya ce: “A wurina, munafukai ne kawai.

Munafikai ne kawai; Sule Lamido ya caccaki gwamnonin APC da ke zawarcin Jonathan
Munafikai ne kawai; Sule Lamido ya caccaki gwamnonin APC da ke zawarcin Jonathan
Source: Facebook

Su, gwamnonin APCn da suke neman sa. Shin babu ya cancanci shugaban kasa a cikin APCn? Wannan ba ƙaramin munafunci ba ne

KARANTA: Za'a yi amfani da jirage masu sarrafa kansu wajen raba magunguna a Kaduna

Lamido ya ce ba wanda ya dace da shugabancin Najeriya sai wanda zai wakilci ƙasar baki ɗaya ba tare da nuna bambancin addini ko kabilanci ba.

Shekarun APC sun kawo ƙiyayya tsakanin yan Najeriya, Najeriya da ta rabu cike ga rashin tsaro tare da al’adar tsanar juna. Abin da jam’iyyar APC ke faɗa a arewa ya bambanta da na Kudu. APC jam’iyya ce ta masu magana biyu" In ji shi.

Legit.ng ta rawaito cewa Rikici ya barke a tsakanin jagororin APC reshen jihar Kwara akan aikin sabunta rijistar zama mamba.

Wasu matasa sun yi yunkurin hana shugaban riko na jam'iyyar APC da shugabar mata su shiga wurin taron jam'iyya.

Rahotanni sun bayyana cewa an farfasa gilashin motar shugabar mata ta jam'iyyar tare da yin awon gaba da wasu kaya mallakinta.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel