An gano wata rigar sarauta da aka rina tun lokacin Annabi Dauda, shekaru 3000 baya

An gano wata rigar sarauta da aka rina tun lokacin Annabi Dauda, shekaru 3000 baya

- An samu wata tsohuwar riga da ake tsammanin tun lokacin Annabi Dauda aka yi mata rinin kalar makuba

- Babban abinda ya bawa jama'a mamaki shine yadda aka samu rigar cikin hayyacinta ba tare da kodau ba

- Na'urar auna dadewar kayayyaki ta nuna cewa rigar ta shafe kimanin shekaru 3000 a duniya

A wata gagarumar tsintuwa, manyan masu bincike a ƙasar Isra'ila sun gano wata rigar sarauta mai shekaru kimanin 3000 tun ta zamanin Annabi Dawuda.

An gano rigar ne wacce saƙa da zaren ulu, a cikin tarin sharar masana'antu a "Slave's Hill," wani wurin da aka taɓa narkar da tagulla a cikin kwarin Timna, kamar yadda BBC ta rawaito.

Wani abin mamaki ma shine yadda aka tsinci rigar da rininta na tsawon shekaru sama da 3,000 ba tare da ta koɗe ba, lamarin da ya baiwa masanan mamaki.

An gano wata rigar sarauta da aka rina tun lokacin Annabi Dauda, shekaru 3000 baya
An gano wata rigar sarauta da aka rina tun lokacin Annabi Dauda, shekaru 3000 baya
Source: Twitter

"Launin shine abinda ya fi jan hankalinmu kuma mun same ta da launin rinin kallar purple tun shekaru aru-aru masu yawa" in ji Farfesa Erez Ben-Yosef na jami'ar Tel Aviv dake tsangayar binciken kayan tarihi.

Na'urar auna shekaru ta tabbatar da cewa rigar ta fi shekara dubu kafin zuwan Annabi Isa (100 BC), inda ya ke nuni da zamanin Annabi Suleiman da wurin Annabi Dawuda.

A kwabakin baya ne Legit.ng ta rawaito cewa Misra, wacce yanzu ake kira 'Egypt', ta sanar da cewa wasu masu binciken ma'adanan karkashin kasa sun bankado wani tsohon tarihi a Saqqara da ke kudancin Cairo.

Masu binciken sun gano wata makabarta a karkashin kasa wacce fitaccen masanin tarihin Egypt, Zahi Hawass, ya ce an ginata ne a matsayin wurin binne Sarauniya Naert.

Sarauniya Naert mata ce wurin Fir'auna Teti, Sarki na farko a gidan masarauta ta 6 da ta mulki kasar Misra.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel