Kwana daya da dira Ogun, Sunday Igboho ya kai wa Fulani hari, shugaban Miyetti Allah

Kwana daya da dira Ogun, Sunday Igboho ya kai wa Fulani hari, shugaban Miyetti Allah

- Shugaban kungiyar Miyetti Allah ya zargi Sunday Igboho da kai hari kan al'ummar Fulani a Ogun

- Ranar Litinin Igboho ya dira jihar Ogun da niyyar korar Fulani

- Ya lashi takobin bi jiha-jiha a kasar Yarabawa domin fitittikan Fulani masu garkuwa da mutane

Mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Adeyemo Igboho, ana zargin ya kai hari wata rugar Fulani dake garin Igua, karamar hukumar Yewa ta Arewa a jihar Ogun, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar makiyaya Miyetti Allah (MACBAN), na jihar Ogun, Alhaji Abubakar Dende, ya bayyanawa manema labarai cewa yanzu haka yaran Sunday Igboho sun banka wuta gidan Sarkin Fulanin Igua, Alhaji Adamu Oloru.

"Sun kona gidajen dake garin da na Sarkin Fulani, Alhaji Adamu Oloru, dake Igua da yamman nan (Litinin)," ya bayyana.

"Bayan haka suka kona kasuwar dabbobi."

"Tun lokacin da muka samu labarin zuwansa muka sanar da jami'an tsaro, har da DSS."

"Hankalinmu a tashe yake saboda bamu da wanda zai karemu."

"Da yawa cikin mutanenmu yanzu sun gudu cikin daji," ya kara.

Alhaji Muhammadu Chede ya bayyanawa Daily Trust cewa an kashe wani bafulace, Jiji Danmawale, kuma aka kona gawarsa.

"Yanzu muna Randa a Abeokuta, muna shirye-shiryen jana'izarsa," yace.

Hakazalika, kwamishanan yan sandan jihar yanzu haka yana ganawa da al'ummar garuruwan da aka kaiwa hari.

KU DUBA: Idan aka rage farashin mai, za'ayi wahalar mai kwanan nan, Ministan Mai

Kwana daya da dira Ogun, Sunday Igboho ya kai wa Fulani hari, shugaban Miyetti Allah
Hoto: dailytrust.com
Kwana daya da dira Ogun, Sunday Igboho ya kai wa Fulani hari, shugaban Miyetti Allah
Source: UGC

DUBA NAN: Hukumar Hisbah ta damke kiret din giya 260 a jihar Bauchi

A bangare guda, Kungiyar Makiyayan Arewa (NEF) ta bayyanawa al'ummar Fulani dake kudancin Najeriya su dawo gida idan ana koransu daga inda suka zaune.

Hakazalika Kungiyar NEF ta yi kiraga gwamnonin Arewa su shirya karban Fulanin dake shirin dawowa gida daga kudu.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa wannan na kunshe cikin jawabind da kakakin kungiyar dattawan, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya saki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel