Idan aka rage farashin mai, za'ayi wahalar mai kwanan nan, Ministan Mai
- Akwai yiwuwan shiga wahalar man fetur kwanan nan, gwamnatin tarayya tace
- Karamin ministan mai, Timipre Sylva, ya bayyana hakan a ganawarsa da shugabannin kwadago
- An yi zaman ne domin hana yajin aiki kan kara farashin man fetur da wutan lantarki
Gwamnatin tarayya ta bayyana yiwuwar wahalar man fetur a fadin tarayya kwanan nan.
Yayin ganawa da shugabannin kungiyoyin kwadago a ranar Litinin, 1 ga Febrairu, Timipre Sylva, karamin ministan mai, ya bayyana cewa da yiwuwan ayi wahalar mai idan yan kwadago suka zake kan cewa lallai sai an rage farashin mai, Channels TV ta ruwaito.
Za'a tuna cewa a Nuwamban 2020, gwamnatin ta sanar da karin farashin man fetur daga N147.67 zuwa N155.17 ga lita, kuma hakan ya tilastawa yan kasuwa sayar da mai ga mutane N165 zuwa N173.
Hakazalika gwamnatin ta kara farashin wutan lantarki duk a lokaci guda.
Amma yayin ganawan ranar Litinin tsakanin gwamnati da wakilan kungiyoyin kwadago karkashin jagorancin shugaban NLC Ayuba Wabba da shugaban TUC, Quadri Olaleye, gwamnati ta gabatar da matsayarta.
Shugabannin kwadagon kuwa suka bukaci a basu makonni uku domin tunani kan bukatar gwamnati.
Shi kuma karamin Ministan mai ya ce sam, idan aka basu makonni uku mai zai yi wahala a kasar.
DUBA NAN: Hukumar Hisbah ta damke kiret din giya 260 a jihar Bauchi
KU KARANTA: Bayan fitowa daga gidan yari, an sake gurfanar da Orji Kalu a kotu
A bangare guda, Ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kashe naira biliyan 2.42 a kan tafiye-tafiye na cikin gida da kasashen ketare a 2021 yayin da fadar shugaban kasa za ta kashe N135.6 miliyan a kan lemuka kamar yadda jaridar The Cable ta gani a kasafin kudi.
A ranar 31 ga watan Disamban 2020 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan kasafin kudin kasar nan na 2021.
A kasafin kudin, jimillar kudin da aka warewa ofishin shugaban kasan na manyan ayyuka shine N3.82bn sai N2.76bn na ayyukan yau da kullum.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng