Hukumar Hisbah ta damke kiret din giya 260 a jihar Bauchi

Hukumar Hisbah ta damke kiret din giya 260 a jihar Bauchi

- Jami'an hukumar Hisbah a Bauchi sun yi babban kamun kwalaben barasa

- Hukumar ta shahara da dabbaka hukunce-hukuncen addinin Musulunci a Arewacin Najeriya

Hukumar Hisbah ta jihar Bauchi ya damke kiret da giya 260 daga gidajen otal da banbadewa a cikin kokarinta na dabbaka dokokin addinin Musulunci.

Kwamishanan Hisban da aiwatar da Shari'a, Aminu Balarabe, ya bayyana hakan yayi bayyana kwalaben giyan da hukumar ta kwace ranar Talata.

Ya ce kiret din giya 216 aka sace a karamar hukumar Misau da kuma kiret 44 a cikin Bauchi da wasu gidajen giya dake Dass Part.

"Za mu cigaba da sanya ido domin damke masu aikata alfasha," yace.

Ya ce zai bukaci kotu a fasa kwalaben giyan saboda dokar shari'a ta 2003 ta haramta sayar da giya da shanta.

Mr Balarabe, wanda ya bayyana kwalaben giyan gaban ofishin hukumar Hisban, ya ce an damke ma'aikatan gidajen giyan shida kuma za'a hukuntasu saboda hakan ya zama izina ga wasu.

"Wuraren da aka amince a sayar da giya sune barikin sojoji da yan sanda, gidajen zoo," yace.

KU DUBA: Jerin manyan jami’an yan sanda da ka iya maye gurbin Adamu a matsayin IGP

Hukumar Hisbah ta damke kiret din giya 260 a jihar Bauchi
Hukumar Hisbah ta damke kiret din giya 260 a jihar Bauchi Credit: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU DUBA: A kula: Yan sanda na iya kama ka a wajen taron jama’a daga ranar 2 ga watan Fabrairu

A bangare guda, Hukumar Hisbah ta Jihar Bauchi ta ce ta kama matasa shida kan zarginsu da hannu wurin shirya casun 'badala' a kauyen Dolam da ke karamar hukumar Tafawa Balewa na jihar.

Aminu Idris, kwamishinan da ke kula da Hisbah da aiwatar da shari'a a jihar ne ya bayyana hakan yayin hira da kamfanin dillancin labarai NAN a ranar Litinin, The Cable ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng