Yanzu-yanzu: Gwamna Zulum ya sallami kwamishanan lafiyan Borno, bai bayyana dalili ba

Yanzu-yanzu: Gwamna Zulum ya sallami kwamishanan lafiyan Borno, bai bayyana dalili ba

- Babagana Zulum ya sallami daya daga cikin kwamishanoninsa

- Gwamnan bai bayyana ainihin dalilin sallaman kwamishanan ba

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sallami kwamishanan lafiya, Dakta Salihu Kwayabura, daga kujerararsa.

Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, ya bayyana hakan ranar talata a Maiduguri, inda yace gwamna Zulum ya yi haka ne don gyara a ma'aikatan kiwon lafiyan jihar.

A jawabin Isa Gusau, Gwamna Zulum ya mika godiyarsa da Dr Salhiu Kwayabura bisa gudunmuwar da ya bada wajen cigaban ma'aikatar lafiyan jihar na kimanin shekaru biyu na mulkinsa.

Gusau ya kara da cewa Gwamna Zulum ya umurci shugaban ma'akatan fadar gwamnatin, Farfesa Hussain Marte, wanda shima masanin kiwon lafiya ne ya kasance kwamishana mai rikon kwarya kafin a nada sabo.

KU KARANTA: Kungiyar CNPP ta yi kira a tsige Ministan labarai Lai Mohammed, da Garba Shehu

Yanzu-yanzu: Gwamna Zulum ya sallami kwamishanan lafiyan Borno, bai bayyana dalili ba
Yanzu-yanzu: Gwamna Zulum ya sallami kwamishanan lafiyan Borno, bai bayyana dalili ba Hoto: @govborno
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan fitowa daga gidan yari, an sake gurfanar da Orji Kalu a kotu

A bangare guda, gwamnatin jihar Borno ta nada Abba Umar Jato a matsayin Shehun Dikwa, Daily Trust ta ruwaito.

Abba Umar Jato ya gaji marigayi Shehu Mohammed Ibn Shehu Masta II El-Kanemi, wanda ya rasu a makon da ya gabata.

Nadin nasa a matsayin mai fada aji na farko da Gwamna Babagana Zulum ya yi ya fito ne a cikin wata sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng