Yanzu yanzu: Tsohon minista Tony Momoh ya rasu

Yanzu yanzu: Tsohon minista Tony Momoh ya rasu

- Jigo a jam'iyyar All Progressives Congress, APC, dan jarida kuma dan siyasa Prince Tony Momoh ya rasu

- Momoh, wanda ya taba rike mukamin ministan sadarwa da al'adu ya rasu ne a ranar Litinin bayan shafe shekaru 82 a duniya

- Wasu fitattun yan Nigeria ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun wallafa sakon ta'aziyyar rasuwarsa

Jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma tsohon ministan sadarwa da al'adu, Prince Tony Momoh ya riga mu gidan gaskiya, Daily Trust ta ruwaito.

Prince Momoh, kwararren dan jarida, ya yi aiki a matsayin ministan Najeriya yayin zamanin mulki na Janar Ibrahim Badamasi Babangida daga shekarar 1986 zuwa 1990.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 82 a duniya.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa aka ga Buhari ba takunkumi a fuskarsa a Daura

Yanzu yanzu: Tsohon minista Tony Momoh ya rasu
Yanzu yanzu: Tsohon minista Tony Momoh ya rasu. Hoto: @TheNationNews
Source: Twitter

Yana daya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar APC mai mulki.

Momoh, wanda dan asalin garin Auchi ne, hedkwatar mulki na karamar hukumar Etsako West na jihar Edo ya rasu ne a ranar Litinin.

KU KARANTA: EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau kan almundahar kwangilar N260m

Tsohon dan jarida ne kuma ya zama shugaban tsohuwar jam'iyyar Congress for Progressive Change, CPC, Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa kafin daga bisani ta yi maja ta zama jam'iyyar APC mai mulki.

Ba a bayyana dalilin rasuwarsa ba a lokacin wallafa wannan rahoton.

Tuni dai wasu manyan yan Nigeria ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar sun yi ta'azziyar rasuwarsa.

A wani labarin daban, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Muhammadu Buhari a shekarar 2015 duk da cewa ya san 'bai san komai ba' Olagunsoye Oyinlola, tsohon gwamnan jihar Osun ya ce.

Mista Oyinlola ya yi bayanin cewa Mista Obasanjo ya yanke shawarar goyon bayan Mista Buhari ne saboda takaicin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Duk da cewa (shi) Obasanjo ya san cewa dan takarar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba zai iya tabuka wani abin azo-a-gani ba, amma duk da haka ya goyi bayansa bayan wasu jiga-jigan yan Najeriya sun matsa masa lamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel