Sabo Nanono: Ministan noma ya fadi dalilin da yasa aikata miyagun laifuka ke karuwa a Nigeria

Sabo Nanono: Ministan noma ya fadi dalilin da yasa aikata miyagun laifuka ke karuwa a Nigeria

-Ministan noma da raya karkara, Sabo Nanono, ya bayyana cewa daina aikin masaku 145 a sassan Nigeria ya kara matsalar rashin tsaro

- Nanono ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, a fadar gwamnatin jiha da ke Lafia

- A cewar Nanono, riko tare da bukasa harkokin noma ne hanyar da zasu kawowa kasa da jama'arta cigaba

Sabo Nanono, ministan harkokin noma da raya karkara, ya bayyana cewa durkushewar masana'antun saka 145 a Legas, Kaduna, Kano, da sauran wasu jihohi shine ke haifar da karuwar manyan laifuka a kasa.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, a fadar gwamnatin jihar da ke Lafia, kamar yadda BBC ta rawaito cewa Daily Trust ta wallafa.

"Durkushewar kamfanonin saka guda 145 a wasu jihohin Nigeria da suka hada da Kaduna, Legas, da Onitsha, da kuma raguwar bukatar audugar da ake nomawa ya haifar da aikata manyan laifuka," a cewarsa.

KARANTA: Afenifere ta bayyana dalilin da yasa Tinubu yake tsoron tunkarar Buhari a kan bahallatsar makiyaya da Yoruba

A cewar ministan, kamfanonin saka ne suka fi daukar ma'aikata a masana'antun da ke fadin kasar nan amma yanzu sun rufe, sun daina aiki.

Sabo Nanono: Ministan noma ya fadi dalilin da yasa aikata miyagun laifuka ke karuwa a Nigeria
Sabo Nanono: Ministan noma ya fadi dalilin da yasa aikata miyagun laifuka ke karuwa a Nigeria
Asali: UGC

Nanono ya kara da cewa rufe masana'antun ya kara talauci a tsakanin jama'a wanda hakan kuma ya jawo karuwar aikata manyan laifuka.

KARANTA: Babban sarkin kabilar Yoruba ya aika muhimmin sako ga 'yan siyasa bayan ganawa da Buhari

Ministan ya bayyana cewa bunkasa harkokin noma tare da farfado da masana'antu ne kadai zai ciyar da kasa da mutane gaba.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa rundunar sojin Nigeria ta jibge dakarunta mata guda 300 a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna domin su bayar da gudunmawa wajen yakar 'yan ta'adda da suka addabi hanyar.

A ranar Laraba ne rundunar soji ta sanar hakan tare da bayyana cewa dakarun mata zasu karawa takwarorinsu maza karfi a kokarinsu na ganin bayan 'yan bindiga a babbar yanyar da kewaye.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ne ya tarbi rukunin farko na dakarun sojin bayan isowarsu Kaduna.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng