Garkuwa da mutane: Hotunan dakarun soji mata 200 da aka jibge a hanyar Abuja-Kaduna

Garkuwa da mutane: Hotunan dakarun soji mata 200 da aka jibge a hanyar Abuja-Kaduna

- Rundunar soji ta tura rundunar dakarunta mata zalla 300 zuwa babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya jagoranci tawagar jami'an gwamnatinsa domin tarbar rundunar sojojin

- El-Rufa'i ya bayyana cewa ganin rundunar matan ya kara masa karfin gwuiwar cewa nan bada dadewa ba batun garkuwa da mutane da sauran aiyukan ta'addanci a hanyar zai kare

Rundunatr sojin Nigeria ta jibge dakarunta mata guda 300 a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna domin su bayar da gudunmawa wajen yakar 'yan ta'addar da suka addabi hanyar.

A ranar Laraba ne rundunar soji ta sanar hakan tare da bayyana cewa dakarun mata zasu karawa takwarorinsu maza karfi a kokarinsu na ganin bayan 'yan bindiga a babbar yanyar da kewaye.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ne ya tarbi rukunin farko na dakarun sojin bayan isowarsu Kaduna.

Garkuwa da mutane: Hotunan dakarun soji mata 200 da aka jibge a hanyar Abuja-Kaduna
Garkuwa da mutane: Hotunan dakarun soji mata 200 da aka jibge a hanyar Abuja-Kaduna @Daily_trust
Source: Twitter

El-Rufa'i ya jagoranci tawagar gwamnatinsa da suka hada da mataimakiyarsa, Hadiza Balarabe, zuwa bakin babbar hanyar da ta shigo garin Kaduna domin yi wa ayarin sojojin maraba.

Yayin da yake gabatar da jawabin yi musu marhabun, El-Rufa' ya bayyana cewa zuwan dakarun ya kara masa karfin gwuiwar cewa nan bada dadewa ba batun 'yan bindigar da suka addabi babbar hanyar zai zama tarihi.

A kwanakin baya Legit.ng ta rawaito shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na cewa ko kadan ba ya jin dadin yadda 'yan ta'adda ke salwantar da rayukan jama'a a sassan Nigeria.

A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi wasu tsare-tsare domin kawo karshen kungiyar Boko haram a cikin shekarar 2021.

Buhari ya lissafa wasu jiga-jigan dalilai guda hudu da zasu bawa gwamnatinsa damar ganin bayan kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin wannan shekarar, 2021.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel