Yanzu yanzu: CAS ta mayarwa Ahmad kujerarsa na shugaban CAF

Yanzu yanzu: CAS ta mayarwa Ahmad kujerarsa na shugaban CAF

- Kotun sauraron korafin wasanni, CAS, ta janye dakatarwar da FIFA ta yi wa shugaban CAF, Ahmad Ahmad

- FIFA ta dakatar da Ahmad daga shiga harkokin wasanni ne kan zarginsa da saba wasu dokoki na hukumar kwallon kafa

- Sai dai a bangarensa Ahmad ya daukaka kara bisa zargin kuma kotun na CAS da dakatar da haramcin da aka masa gabannin sabon zaben shugaban CAF

Kotun harkokin wasanni, CAS, ta mayar da Ahmad Ahmad na kasar Madagascar kan kujerarsa na shugabancin Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF, biyo bayan wani hukunci da kotun wasanni ta yanke, The Punch ta ruwaito.

Hukumar Kwallon kfsa ta kasa da kasa, FIFA, a watan Nuwamba ta haramtawa Ahmad shiga wata harka ta kwallon kafa bayan samunsa da saba dokoki da dama na kwallon kafa.

Sai dai Ahmad ya daukaka kara a kan wannan hukuncin inda a ranar Juma'a aka sake yanke hukunci.

DUBA WANNAN: Shekau ya fitar da sabon sautin murya, ya gargadi sabbin shugabanin sojoji da Buhari ya naɗa

Yanzu yanzu: CAS ta mayarwa Ahmad kujerarsa na shugaban CAF
Yanzu yanzu: CAS ta mayarwa Ahmad kujerarsa na shugaban CAF. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Sai dai duk da haka Ahmad bai cancanci ya shiga takarar shugabancin CAF ba a zaben da za a yi a watan Maris tunda matakin na CAS ya zo ne bayan hukumomin FIFA da CAF sun yi taro a makon da ya gabata don bita cancantar wadanda ke neman yin takara.

CAF ta ce za ta saurari cikaken daukaka karar da Ahmad ya yi a ranar 2 ga watan Maris sannan ta yanke hukunci kafin zaben shugaban CAF da za a yi a ranar 12 ga watan Maris.

KU KARANTA: Wadanda Buhari ya naɗa manyan hafsoshin sojoji sun cancanta, in ji Shettima

"Saboda irin cutarwa da za a yi wa Mr Ahmad idan ba a janye hukuncin da kwamitin ladabtarwa ta yi masa ba kafin zaben CAF, kwamitin CAF ta amince da bukatar janye dakatarwar da FIFA ta yi masa," a cewar CAS, cikin wata sanarwa da ta fitar.

An janye dakatawar da FIFA ta yi masa har zuwa ranar da CAS za ta zartar da hukunci kan lamarin.

Tunda yana karkashin dakatarwa a ranar Alhamis a lokacin da FIFA ta yi taro, ana ganin Ahmad bai cancanta ya shiga takarar ba.

Yanzu yana bukatar kotun ta sake yin wani hukunci don hallarta masa shiga takarar.

A wannan makon, mutane hudu da ke neman takarar shugabancin CAF a zaben da za ayi a 12 ga watan Maris sun hada da Jacques Anouma (Ivory Coast), Patrice Motsepe (South Africa), Augustin Senghor (Senegal), Ahmed Yahya (Mauritania).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164