Mambobin jam'iyyar APC 5,000 sun sauya sheka jam'iyyar PDP

Mambobin jam'iyyar APC 5,000 sun sauya sheka jam'iyyar PDP

- Jam'iyyar PDP ta samu babban karuwa a garin Michika, jihar Adamawa

- Wannan ya biyo bayan fitan manyan jiga-jigan PDP daga jam'iyyar zuwa APC

Shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Michika, jihar Adamawa da wasu mambobin jam'iyyar 5000 sun sauya sheka jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Mista John Fave wanda ya jagoranci masu sauya shekar ya ce sun koma PDP ne domn taimakawa jam'iyyar, Jaridar Leadership ta ruwaito.

Shugabannin jam'iyyar sun hada shugaban APC na karamar hukumar, tsohon dan majalisar wakilai,, Mista James Ijai, da wasu shugabannin jam'iyyar a gunduma-gunduma 10.

Shugabannin sun zo tare da magoya baya da yawa.

Yayin magana a hira da manema labarai a Yola, mai magana da yawun masu sauya sheka, Emmanuel Ijarafu, ya ce sun yanke shawara fita daga APC ne saboda irin namijin aikin da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ke yi a jihar.

Shugaban APC na karamar hukumar Michika, John Fave, ya bayyana cewa rashin adalcin da ake a APC ne ya wajaba masa barin jam'iyyar.

KU KARANTA: COVID-19 ta shiga jerin kalubalen duniya kamar ta'addanci, rashawa, in ji Buhari

Mambobin jam'iyyar APC 5,000 sun sauya sheka jam'iyyar PDP
Mambobin jam'iyyar APC 5,000 sun sauya sheka jam'iyyar PDP
Asali: UGC

KU KARANTA: Buratai ya mika mulki ga sabon shugaban hafsan sojin kasa, Ibrahim Attahiru (Hotuna)

A bangare guda, Gani Adams, Aare Ona Kakanfo na kasar Yarbawa, ya ce tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) "na shaidan ne kuma na miyagu".

Adams ya fadi haka ne a ranar Laraba lokacin da yake gabatarwa a shirin Siyasar Yau, shirin gidan Talabijin na Channels.

Aare Ona kakanfo na kasar Yarbawa ya ce ana tafiyar da kasar ne bisa tsari mara kyau.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng