2023: Wata kungiyar Musulunci ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu

2023: Wata kungiyar Musulunci ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu

- Kungiyar kare hakkin musulmai (MURIC) ta bayyana yadda take goyon bayan Bola Tinubu yayi mulki a 2023

- Shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya ce babu shugaba mai nagartar da ya dace da mulkin Najeriya kamar Tinubu

- Ya kara da rokon kaf yarabawan dake Najeriya da su hada karfi da karfe wurin ganin sun dunkule wuri guda don mara masa baya

Kungiyar kare hakkin musulmai (MURIC) ta bayyana goyon bayanta dari bisa dari ga jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, don ya gaji shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Kamar yadda darektan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola yace, Asiwaju Tinubu yana da duk wasu halaye da dabi'u da suka dace shugaban kasa ya mallaka.

A wata takarda, Akintola ya yaba wa masu ruwa da tsakin jihar Oyo da suka yi gaggawar dakatar da fadan Hausa/Fulanin garin Igangan na Ibarapa, jihar Oyo da Yarabawansu, inda yace wajibi ne Yarabawa su hada kawunansu don samun mulki a 2023.

KU KARANTA: Arangamar kungiyoyin 'yan bindiga biyu ya kawo salwantar rayukan 'yan ta'adda masu yawa a Katsina

2023: Wata kungiyar Musulunci ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu
2023: Wata kungiyar Musulunci ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu. Hoto daga @Thenation
Asali: UGC

Ya roki sauran Yarabawa na kasar nan da su dakatar da duk wata gaba ko hamayya dake tsakaninsu don su cimma burinsu na mulki a 2023, The Nation ta wallafa.

Ya bayyana yadda kaf Yarabawa ba ya ganin wani yana da halaye da nagartar da ya cancanci yayi mulki kamar tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu.

Ya kara da cewa, ya dace duk su hada kawunansu wurin ganin sun tsayar da shi ya samu mulkin Najeriya a 2023.

KU KARANTA: Dangote: Yadda tsohuwar budurwata ta so 'warwarar' $5m daga wurina

A wani labari na daban, majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta bai wa sabbin hafsoshin soji da ya nada wa'adin kawo karshen matsalar tsaro, garkuwa da mutane, 'yan bindiga da sauran kalubalen tsaron da suka addabi kasar nan.

A yayin zantawa da manema labarai a Abuja a jiya, shugaban kwamitin majalisar a kan harkokin sojoji, Sanata Ali Ndume, ya ce idan Buhari ya samar da abubuwan bukata ga sabbin hafsoshin tsaro, ya basu wa'adi a kan aikin da yake so su yi.

Kamar yadda yace, kada gwamnati ta bata lokaci wurin maye gurbinsu da wasu idan suka gaza, Vanguard ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel