Hukumar kula da sadarwa NCC ta fara gudanar da bincike kan saurin karewan 'Data'

Hukumar kula da sadarwa NCC ta fara gudanar da bincike kan saurin karewan 'Data'

- Bayan rage farashin Data, yan Najeriya sun koka kan saurin karewarta

- Hakazalika anyi korafe-korafen kwashe wa mutane kudi waya

- Hukumar NCC ta lashi takobin gano gaskiyar abinda ke faruwa

Hukumar kula da sadarwan Najeriya NCC ta bayyana cewa ta kaddamar da bincike kan kararrakin da ake shigarwa kan saurin karewan Data da kwashewa mutane kudi a waya.

Shugaban hukumar NCC, Farfesa Umar Danbatta, a ranar Alhamis ya bayyana haka a wani taron bashi lambar girma da mujallar MoneyReport ta bashi a matsayin jarumin 2020 a Abuja.

Danbatta ya ce hukumar na iyakan kokarinta wajen ganin cewa kamfanonin sadarwa ba sa cutan jama'a.

Ya ce ta wannan bincike na hukumar ke gudanarwa, "za'a gani takamammen dalilin da yasa Data ke saurin karewa da mutane ke fuskanta da kuma kwashewa mutum kudi da bai dace ba."

"Mun bayyana cewa duk da rage farashin data, sai an cigaba da binciken kuma an nunawa kamfanonin sadarwa sakamakon binciken," Danbatta yace.

Danbatta ya yi kira ga yan Najeriya suyi hakuri yayinda ake gudanar da binciken saboda hukumar za ta tabbatar da cewa kamfanonin sun yi abinda ya dace domin jin dadin kwastamomi.

KU KARANTA: COVID-19 ta shiga jerin kalubalen duniya kamar ta'addanci, rashawa, in ji Buhari

Hukumar kula da sadarwa NCC ta fara gudanar da bincike kan saurin karewan 'Data'
Hukumar kula da sadarwa NCC ta fara gudanar da bincike kan saurin karewan 'Data' Credit: @FMoCDENigeria
Source: Facebook

KU KARANTA: Bincike ya nuna wiwi zai iya rage yiwuwar kamuwa da cutar COVID-19

A bangare guda, gwamnatin tarayya a ranar Alhamis tace an rage kudin 'Data' da kashi 50% bisa umurnin da aka baiwa hukumar sadarwan Najeriya NCC.

Saboda haka, kudin 'Data' na 1GB ya sauko daga N1000 zuwa N487 daga yanzu ( tun watan Nuwamba), The Nation ta ruwaito.

'Data' kudi ne da mutum ke saya a domin amfani da samun shiga yanar gizo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel