Buratai ya kafa tarihi, ya zama shugaban hafsan soji da yafi dadewa kan mulki

Buratai ya kafa tarihi, ya zama shugaban hafsan soji da yafi dadewa kan mulki

- Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabbin hafsoshin tsaro ranar Talata, 26 ga Junairu

- Jawabi daga shugaban kasan, ya ce tsaffin Sojojin sun yi murabus ne daga kujerunsu

- Sakamakon haka, Laftanan Janar Tukur Buratai ya kafa tarihin shugaban hafsoshin sojoji a Najeriya mafi dadewa a tarihi

Sakamakon sallaman Laftanan Janar Tukur Buratai matsayin shugaban hafsoshin Sojin Najeriya ranar Talata, ya zama babban hafsa mafi dadewa kan kujerar mulki a tarihin Najeriya.

Daily Trust ta bayyana cewa Janar Buratai dan asalin jihar Borno ya yi watanni 66 matsayin shugaban Sojojin kasan Najeriya.

Daga Buratai sai marigayi Janar Sani Abacha wanda yayi watanni 60 kan kujerar.

Bayan Abacha, Janar David Ejoor ya yi watanni 56, sai Janar TY Danjuma wanda yayi watanni 51, da kuma Janar Azubuike Ihejirika wanda yayi watanni 40.

Daga cikin wadannan, Janar TY Danjuma da Azubuike Ihejirika kadai suke raye yanzu.

DUBA NAN: Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya (Hotuna)

KU KARANTA: Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya kamu da cutar Korona

Mun kawo muku jiya cewa bayan kiraye-kiraye daga yan majalisun tarayya da manyan masu ruwa da tsaki a Najeriya suka yiwa shugaba Buhari ya sallami hafsoshin tsaro kuma ya nada wasu, Buhari ya amsa a yau.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami dukkan hafsoshin tsaron Najeriya a ranar Talata, 26 ga watan Junairu, 2021, kuma ya nada sabbi ba tare da bata lokaci ba.

Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel