Kimanin yan Najeriya 400 da suka makale a Saudiyya sun dawo gida (Hotuna)

Kimanin yan Najeriya 400 da suka makale a Saudiyya sun dawo gida (Hotuna)

- Bayan kuka da suka kaiwa gwamnatin Najeriya, an dawo da mata da maza kimanin 400 Najeriya daga saudiyya

- An tsaresu a can bisa zargin zama a kasar ba bisa ka'ida ba

- Daga cikinsu akwai mata 83, maza 300 da jariri guda

Yan Najeriya 384 cikin 802 da suka yi kuka ga gwamnatin Najeriya ta cecesu daga kasar Saudiyya inda suka makale sun dira gida Najeriya ranar Alhamis, 28 ga Junairu, 2021.

Hukumomi sun ce za'a killacesu na tsawon wani lokaci kafin a mayar da su jihohinsu.

Sauran 418 kuma ana sa ran dawowansu ranar Juma'a.

Kimanin yan Najeriya 400 da suka makale a Saudiyya sun dawo gida (Hotuna)
Kimanin yan Najeriya 400 da suka makale a Saudiyya sun dawo gida (Hotuna) Credit: BBC
Source: Facebook

Kimanin yan Najeriya 400 da suka makale a Saudiyya sun dawo gida (Hotuna)
Kimanin yan Najeriya 400 da suka makale a Saudiyya sun dawo gida (Hotuna) Credit: BBC
Source: Facebook

KU DUBA: An sake yiwa Alhaji Atiku Abubakar rigakafin Korona a karo na biyu

Kimanin yan Najeriya 400 da suka makale a Saudiyya sun dawo gida (Hotuna)
Kimanin yan Najeriya 400 da suka makale a Saudiyya sun dawo gida (Hotuna) Credit: BBC
Source: Facebook

KU DUBA: Najeriya ta zama kasa ta 2 mafi rashawa a Afrika ta yamma

Mun kawo muku cewa ana sa ran wasu 'yan Najeriya 802 da suka makale a masarautar Saudiyya za su sauka a Abuja yau da gobe.

An tsare su a wurare daban-daban da ake tsare mutane a Saudiyya kan batun kaura ba bisa ka'ida ba.

Sakataren din-din-din na Ma’aikatar Harkokin Waje, Gabriel Aduda, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce za a karbi wadanda za su dawo din ne a Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, ta hanyar jiragen sama biyu na Saudiyya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel