Dumbin masu zanga-zangar ENDSARS sun dawo suna 'romon baka' akan aikin dan sanda
- IGP Mohammed Adamu, babban sifeton rundunar 'yan sanda ya tona asirin wasu matasa da suka gudanar da zanga-zangar ENDSARS
- An gudanar da zangar-zangar ENDSARS ne a shekarar 2020 domin nuna adawa da zaluncin 'yan sanda da neman a rushe rundunar SARS
- Zangar-zangar, wacce aka fara a matsayin ta lumana, ta rikide zuwa kazamin rikici a jihohin da ta samu karbuwa a sassan Nigeria
Babban sifeton rundunar 'yan sandan Nigeria, IGP Mohammed Adamu, ya bayyana cewa akwai dumbin matasan da suka gudanar da zanga-zangar ENDSARS a cikin masu neman aikin dan sanda.
A cikin watan Oktobar shekarar 2020 ne aka fara gudanar da zanga-zangar ENDSARS ta nuna adawa da neman a rushe rundunar 'yan sandan SARS.
Zanga-zangar ENDSARS, wacce aka fara a matsayin ta lumana, ta rikide zuwa rikicin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiya.
Da yake magana a gidan talabijin din Channels yayin wata hira da shi, IGP Adamu ya bayyana cewa wasu daga cikin matasan da suka gudanar da zanga-zangar suna daga cikin masu neman a daukesu aikin dan sanda.
"Da dama daga cikinsu sun dawo suna neman aikin dan sanda, har roko suke yi a taimaka a daukesu aikin dan sanda tare da yin romon bakan cewa aikin Allah ne.
A kwanakin baya Legit.ng ta rawaito shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na cewa ko kadan ba ya jin dadin yadda 'yan ta'adda ke salwantar da rayukan jama'a a sassan Nigeria
A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi wasu tsare-tsare domin kawo karshen kungiyar Boko haram a cikin shekarar 2021.
Buhari ya lissafa wasu jiga-jigan dalilai guda hudu da zasu bawa gwamnatinsa damar ganin bayan kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin wannan shekarar, 2021.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng