Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya (Hotuna)

Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya (Hotuna)

Bayan kiraye-kiraye daga yan majalisun tarayya da manyan masu ruwa da tsaki a Najeriya suka yiwa shugaba Buhari ya sallami hafsoshin tsaro kuma ya nada wasu, Buhari ya amsa a yau.

Wadanda shugaba Muhammadu Buhari ya nada sune, Manjo Janar Leo Irabor wanda zai maye gurbin Janar Gabriel Olonisakin (Shugaban hafsoshin tsaro), da Manjo Janar Ibrahim Attahiru wanda zai maye Laftanan Janar Tukur Buratai (Shugaban Sojin kasa).

Sauran sune AVM Isiaka Amao wanda zai maye gurbin Air Marshal Sadique Baba (Shugaban mayakan sama), sannan · Rear Admiral A.Z Gambo (shugaban sojojin ruwa) wanda zai maye gurbin Ibok Atas.

Ga wasu abubuwan da ya kamata ku sani game da sabbin hafososhin tsaron:

Manjo Janar Leo Irabor (Chief of Defence Staff)

Manjo Janar Irabor ya zo daga Agbor, jihar Delta kuma yana cikin jerin daliban 39 Regular Course da sukayi karatu a makarantan Soji

Ya yi kwamandan horaswa na hukumar Soji.

Ya yi kwamadan rundunar Operation Lafiya Dole da kuma kwamandan rundunan hadaka MNJTF a Chadi.

Kwararran Injiniya ne.

Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya (Hotuna)
Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya (Hotuna)
Source: UGC

Air Vice Marshal Isiaka Amao

An haifi Air Vice Marshal Isiaka Amao a 14 ga Satumba, 1965 a Enugu, amma dan asalin jihar Osun ne.

Ya shiga hukumar mayakan sama a ranar 19 ga Junairu, 1984.

Ya rike mukamin mataimakin mai bada shawara kan tsaro a ofishin jakadancin Najeriya dake Landan, mataimakin diraktan ayyuka a hedkwatar tsaro, sannan yayi diraktan shirye-shirye a hukumar sojin sama.

Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya (Hotuna)
Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya (Hotuna)
Source: UGC

· Manjo Janar I. Attahiru

Gabanin nadin da aka yiwa Attahiru Ibrahim yau, ya kasance GOC 82Div.

Ya yi kwamandan Operation Lafiya Dole a Mayun 2017 amma aka tsigeshi saboda ya gaza kamo Abubakar Shekau bayan wa'adin kwanaki 40 da shugaban hafsan soji na lokacin, Yusuf Buratai, ya bashi.

Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya (Hotuna)
Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya (Hotuna)
Source: UGC

· Rear Admiral A.Z Gambo

An haifi Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo a ranar 22 ga Afrilu 1966 a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

Ya shiga makarantan Sojin ruwa ranar 24 ga Satumba 1984.

Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya (Hotuna)
Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya (Hotuna)
Source: UGC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel