N600,000 nike sayarwa yan bindigan Katsina AK47, Mai fataucin makamai

N600,000 nike sayarwa yan bindigan Katsina AK47, Mai fataucin makamai

- Jami'an yan sanda sun damke kasurgumin mai safarar makamai

- Mutumin ya bayyana farashi da adadin bindigogin da yake sayarwa yan bindiga

- Mutumin ya bayyana ta inda yake shigo da makaman Najeriya da kasar waje

Wani kasurgurmin mai fataucin makamai, Haruna Yusuf, dan garin Sawarya a karamar hukumar Kaita ta Katsina, a ranar Litinin ya bayyana adadin bindigogin da ya sayarwa yan bindiga a jihar.

Yusuf ya ce bindigogi kirar AK47 guda 20 ya sayar a farashin N600,000 ga yan bindiga.

Mutumin, wanda ke cikin masu fataucin makaman da aka gurfanar ya kara da cewa ya sayar da motocin yaki GPMG a farashin milyan hudu.

Ya tabbatar da cewa ya sayi wadannan makamai ne daga wajen wani Hussaini, dan garin Damagaram a jamhuriyyar Nijar kuma ya shigo da su Najeriya ta jihar Katsina.

Bayan damkeshi a gidansa dake kauyen Sawarya da harsasai baro jiragen sama 179, ya ce banda bindigogin, ya sayar da harsasai sama da 5,000 ga yan bindiga.

Yace: "Na sayar da bindigogin AK47 guda 20 kowanne a farashin N600,000. Ina sayansu daga wani Hussaini daga Damagaram, jamhuriyar Nijar sannan in shigo da su Katsina da motar abokina."

KU DUBA: Wadanda suka kona min gida zasu haukace cikin kwana 2, Sunday Igboho

N600,000 nike sayarwa yan bindigan Katsina AK47, Mai fataucin makamai
N600,000 nike sayarwa yan bindigan Katsina AK47, Mai fataucin makamai
Source: Twitter

DUBA NAN: Sifeto Janar na yan sanda ya bada umurnin kama mutumin da ya kori Fulani a Oyo

A bangare guda, a ranar Litinin, 25 ga watan Junairu, 2021, Alhaji Lai Mohammed, ya ce dakarun sojojin kasa sun hallaka ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda 158.

Ministan yada labarai da al’adun Najeriya ya ce dakarun sojojin sun yi wannan namijin kokari ne daga farkon shekarar nan ta 2021 zuwa yanzu.

A cewar Mai girma Ministan, sojojin sun samu wannan nasara ne bayan an fito da sababbin dabaru, jaridar The Nation ta fitar da wannan rahoto.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel