Sifeto Janar na yan sanda ya bada umurnin kama mutumin da ya kori Fulani a Oyo

Sifeto Janar na yan sanda ya bada umurnin kama mutumin da ya kori Fulani a Oyo

- Bayan bukatar da gwamnan jihar Oyo yayi na a damke Sunday Igboho, IGP ya ce a rike shi

- Sunday Igboho ya bukaci dukkan Fulanin dake garin Ibarapa su kwashe inasu-inasu su bar garin

- Sarkin Fulanin jihar yace an kona masa gida kuma an fitittiki iyalansa

Sifeto Janar na yan sanda, IGP Mohammed Adamu, ya bada umurnin damke Sunday Adeyemo, wani mai rajin kafa kasar Oduduwa wanda akafi sani da Sunday Igboho, kan umurnin korar Fulani daga jihar Oyo.

BBC Hausa ta ruwaito Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, da cewa lallai Sifeto Janar ya bada umurnin ranan Juma'a.

Garba Shehu ya ce Sifeto Janar ya bada wannan umurni ne ga Ngozi Onadeko, kwamishanan yan sandan jihar Oyo.

Ya ce a damkeshi kuma a kaishi Abuja.

Kakakin hukumar yan sanda, Frank Mba, bai amsa kiran wayansa ba yayinda akayi kokarin jin ta bakinsa.

DUBA NAN: Amfanin bude makarantu ya rinjayi tsoron kamuwa da Korona, shugaban NCDC

Sifeto Janar na yan sanda ya bada umurnin kama mutumin da ya kori Fulani a Oyo
Sifeto Janar na yan sanda ya bada umurnin kama mutumin da ya kori Fulani a Oyo
Source: UGC

KU KARANTA: Wa'adin korar Fulani daga dazukan Ondo: Gwamnan ya bada umurnin daukan jami'an Amotekun da yawa

Mun kawo muku cewa wani mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Adeyemo Igboho, a ranar Juma'a ya dira Igangan, karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo kamar yadda yayi alkawari.

Ya jaddada cewa Fulani mazauna jihar su tattara inasu-inasu su bar jihar da kasar Yarabawa muddin aka cigaba da garkuwa da mutane.

A makon jiya, Igboho ya kai ziyara unguwar Fulani dake Igangan, inda ya basu kwanaki bakwai su fita daga garin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel