Hotunan auren yara 2 da karya bayan sun fara fitar da hakora ta dasashin sama

Hotunan auren yara 2 da karya bayan sun fara fitar da hakora ta dasashin sama

- Wasu iyaye sun aurar da yaransu biyu maza ga karya bayan sun fara hakori ta dasashin sama

- Wannan fitacciyar al'ada ce da ake yi a kabilar Ho domin korar miyagun aljanu daga yaran

- Karyar tana lashe kafafun dangin angunanta biyu domin nuna girmamawa garesu baki daya

An aurar da yaro mai rarrafe da wani mai shekaru 6 ga karya bayan sun fara yin hakora ta dasashin sama wanda ake alakantawa da babban abu mara kyau.

Fara fitar hakora ta dasashin sama ana alakanta shi da mugun abu a yankin Mayurbhanj da ke kasar India, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Kabilar Ho tana bin wata al'adar camfi ta hanyar aurar da yara kanana ga karya daya a matsayin amaryar yara biyu.

Hotunan auren yara 2 da karnuka bayan sun fara fitar da hakora ta dasashin sama
Hotunan auren yara 2 da karnuka bayan sun fara fitar da hakora ta dasashin sama. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Dubun wasu 'yan bindiga ta cika a dajin Chikwale da ke Kaduna

Kamar yadda New Indian Express ta wallafa, an yi auren ne a kauyen Dadusahi kusa da Sukruli a ranar Juma'a, 22 ga watan Janairun 2021.

An gano cewa iyayen yaran tare da shugaban kauyen sun yi hakan ne domin fatattakar miyagun aljanu daga jikin kananan yaran.

Hotunan auren yara 2 da karnuka bayan sun fara fitar da hakora ta dasashin sama
Hotunan auren yara 2 da karnuka bayan sun fara fitar da hakora ta dasashin sama. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

An gano cewa ana wannan al'adar a kauyen tun fil azal.

Noren Purity ne ya daura auren yaran bayan jama'ar kauyen sun taru yayin da dukkan kabilun da suka yadda da hakan ke kallo.

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna ta bayyana ranar komawa makarantun gaba da sakandare na jihar

Mahaifiyar daya daga cikin yaran ta sanar da Kaling TV: "An daura auren ne saboda zai share dukkan wata la'anta da ka iya fadawa yaran da mu kanmu."

A yayin aure, iyalan amaryar wadanda karnuka ne suna lashe kafar bakin a matsayin nuna girmamawa.

Hotunan auren yara 2 da karnuka bayan sun fara fitar da hakora ta dasashin sama
Hotunan auren yara 2 da karnuka bayan sun fara fitar da hakora ta dasashin sama. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Bayan kammala bikin, 'yan kabilar sun hanzarta zuwa wurin inda suka dinga shafa kan amaryar.

Sun je da wata giya da ake yi daga shinkafa mai suna Handia. An zagaya da yaran fadin kauyen yayin da jama'a ke rawar wata waka da ake kira Madal.

Duk da karya ce amaryar, ana tsammanin angon ya samar da wasu kudi gareta domin shagalin bikin.

A wasu al'adu, ana kiran wannan kudin da sadaki.

A wani labari na daban, a ranar Alhamis rundunar sojin Najeriya tace tana samun nasarori, kuma tana dab da kawo karshen ta'addanci da rashin tsaro a kasar nan.

Kakakin rundunar soji, Manjo janar John Enenche ya sanar da hakan a wani taro a Abuja. Enenche ya bayar da misalin yadda suka ci karfin ta'addanci a jihar Zamfara da Katsina.

A wata takarda ta ranar Litinin, Enenche ya sanar da yadda rundunar Operation Hadarin Daji ta kashe a kalla 'yan bindiga 35 a jihar Zamfara a karon batta guda biyu da suka yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel