Babu wanda ya bawa makiyaya wa'adin barin Kudu maso Yamma, in ji NGF
- Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ce gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu bai bada umurnin korar makiyaya daga jiharsa ba
- Shugaban kungiyar, gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi ya ce gwamnan na Ondo ya umurci makiyaya da ke kiwo a dazukan jihar su tafi suyi rajista ne kawai
- Fayemi ya ce kafafen watsa labarai ba su fahimci abinda gwamnan ke nufi bane inda ya ce bata gari ake neman kora ba makiyaya fulani ba
Kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, ta ce babu wanda ya bawa makiyaya wa'addin ficewa daga jihar Ondo ko wani sashi na yankin Kudu maso Yamma a kasar, The Nation ta ruwaito.
Ta ce ba a fahimci jawabin da gwamnan Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya yi bane a kafafen watsa labarai inda ta ce gwamnan yana magana ne da wadanda ke kiwo a filayen gwamnati da suyi rajista.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun harbi babban odita na jihar Bauchi, sun yi awon gaba da dansa
Shugaban NGF kuma gwamnan Jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi, ya yi magana a Akure yayin taron da suka yi da shugabannin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN).
Dakta Fayemi ya ce jawabin ne gwamnan da ba a fahimta ba ce ta janyo matsalolin da aka samu a Oyo da ya bayyana a matsayin lamari mara dadi.
KU KARANTA: Ka hukunta shugabannin APC da suka aikata laifuka, PDP ta roki Biden
Ya ce Akeredolu ba cewa ya yi makiyaya su fice daga jiharsa ba kawai cewa ya yi makiyayan da ke son su rika kiwo a filayen gwamnati su tafi su yi rajista.
Gwamnan na jihar Ekiti ya ce bata gari su ke kokarin fatattaka ba makiyaya fulani ba.
A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.
An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.
Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng