Tsohon ministan Buhari ya rasu a cibiyar killace masu cutar Korona

Tsohon ministan Buhari ya rasu a cibiyar killace masu cutar Korona

- Tsohon ministan shari'a kuma tsohon ministan ilimi da kimiyya da fasaha, Abdullahi Ibrahim, ya rasu

- Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta sanar da manema labarai cewa tsohon ministan ya rasu ne a cibiyar killace masu cutar korona

- Marigayin ne ministan shari'a a lokacin da gwamnatin mulkin soja a karkashin Janar Abdulsalami Abubakar ta mika mulki ga dimokradiyya a 1999

Abdullahi Ibrahim, tsohon ministan Shari'a Kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, ya rasu a cibiyar killace masu cutar korona da ke Abuja.

Marigayi Ibrahim ya rasu ne ranar Lahadi bayan kamuwa da cutar korona mai sarke numfashi ta hanyar kumbura hunhun mutane.

BBC Hausa ta rawaito cewa marigayin ya taba rike mukamin ministan shari'a, sojin sama da sufuri, a lokacin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na soja.

KARANTA: Hare-hare akan makiyaya: Miyetti Allah ta bawa gwamnatin tarayya shawara a fusace

A cewar BBC, wanda ya sanar da jaridun Nigeria labarin mutuwar tsohon ya nemi a boye sunansa.

Kazalika, an wallafa sanarwar marigayin a shafinsa na yanar gizo, kamar yadda BBC ta wallafa.

Tsohon ministan Buhari ya rasu a cibiyar killace masu cutar Korona
Tsohon ministan Buhari ya rasu a cibiyar killace masu cutar Korona
Asali: Twitter

Marigayin ne ministan shari'a a lokacin da gwamnatin soja a karkashin Janar Abdulsalami Abubakar ta mika mulki mulki ga gwamnatin farar hula ta Obasanjo a shekarar 1999.

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

Kafin ya rike mukamin ministan shari'a, marigayi Ibrahim ya taba rike mukamin ministan ilimi da kimiyya da fasaha.

Marigayi Ibrahim ya shiga jerin sahun manyan mutanen da annobar korona ta ga bayansu a Nigeria tun farkon barkewar ta a shekarar 2020.

A baya Legit.ng Hausa ta rawaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta cafke Malam Ibrahim Tukur, mataimakin shugaban makarantar sakandire, bisa zarginsa da yi wa daya daga cikin dalibansa ciki.

An kama Malam Ibrahim ne bayan dalibar da ya yi wa ciki, mai shekaru goma sha biyu, ta haihu, amma ta hanyar yi mata tiyatar zaro jariri.

A ranar Laraba ne rundunar 'yan sanda ta yi holin masu laifuka daban-daban, cikinsu har da Malam Ibrahim.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel