Fitittikan Fulani daga kasar Yarbawa: Kama da ni idan ka isa, Igboho ga gwamnan Oyo

Fitittikan Fulani daga kasar Yarbawa: Kama da ni idan ka isa, Igboho ga gwamnan Oyo

- Sunday Igboho ya yi fito na fito da gwamnan jiharsa na Oyo

- Igboho ya caccaki gwamnan a kaikace idan yace sun suka taimaka masa ya ci zabe

Dan rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Igboho, ya kalubalanci gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya kama idan ya isa kan barazanar korar Fulani daga jihar da yayi.

A wani bidiyo da ya bayyana ranar Juma'a, Igboho ya caccaki gwamna Makinde, The Nation ya ruwaito.

Duk da cewa bai ambaci sunan gwamnan ba, ya yi kalaman hannunka mai sanda.

Ya tuhumci gwamnan da goyon bayan yan bindigan, inda ya tunawa gwamnan cewa su suka taimaka masa wajen zabe a 2019.

A cewarsa: "Za ka iya kawo dukkan Fulani kasar Yoruba, idan ka ga dama, ku matsiyata. Allah ya tsine muku."

"Kana min barazana a kasata don wasu Fulani. Allah ya tsine maka."

"Shin Fulani ke kafa dokokin kasa ne? Ko ka manta yadda ake bani kudi lokacin da kake neman kujeran gwamna da kuma dukkan abubuwan da na maka lokacin zabe, yanzu kuma kana min barazana?"

KU KARANTA: Da’awar zaman lafiya: Malaman Kirista na arewa sun jinjinawa Sheikh Gumi

Fitittikan Fulani daga kasar Yarbawa: Kama da ni idan ka isa, Igboho ga gwamnan Oyo
Fitittikan Fulani daga kasar Yarbawa: Kama da ni idan ka isa, Igboho ga gwamnan Oyo Credit: @Seyiamakinde @OduduwaRepublic
Asali: Twitter

KU DUBA: Gwamnati ta yi rabon N619.34bn a matsayin kason FAAC a Disamban bara

Mun kawo muku rahoton cewa Sunday Adeyemo Igboho, a ranar Juma'a ya dira Igangan, karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo kamar yadda yayi alkawari.

Duk da cewa bai yaki Fulanin dake zaune a garin ba kamar yadda akayi yada a kafafen sada zumunta, ya jaddada cewa Fulani mazauna jihar su tattara inasu-inasu su bar jihar da kasar Yarabawa muddin aka cigaba da garkuwa da mutane.

A makon jiya, Igboho ya kai ziyara unguwar Fulani dake Igangan, inda ya basu kwanaki bakwai su fita daga garin.

Ya tuhumci yan kabilar Fulani dake yankin da laifin garkuwa da mutane, kashe-kashe, da wasu ayyulan alfasha a garin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel