Korona ta kashe sama da mutane 80 cikin mako guda, sabbin mutane 1,301
- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara
- Kusan makonni biyu a jere, yan Najeriya sama da 1000 ke kamuwa da Korona kullum
- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake kafa dokar hana fita idan adadin ya cigaba da karuwa
Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya ce kawo yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya yanzu ya zarce 112,000 cikin samfuri milyan daya da aka gwada.
Mutane 1,301 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Talata, 18 ga watan Junairu 2021, kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.
Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 113,3015 a Najeriya.
Daga cikin mutanen da suka kamu, an sallami 91,200 yayinda 1464 suka rigamu gidan gaskiya.
Ga jerin wadanda suka kamu a jihohi ranar Litinin:
Lagos-551
FCT-209
Oyo-83
Plateau-65
Kaduna-64
Enugu-61
Rivers-44
Ondo-39
Benue-37
Akwa Ibom-31
Kano-19
Delta-18
Gombe-18
Ogun-16
Edo-15
Kebbi-10
Ebonyi-9
Jigawa-4
Osun-3
Zamfara-3
Borno-1
Nasarawa-1
KU KARANTA: Daga yanzu mutum ko alamun Malaria yake da shi kawai Korona ne, gwamnan Legas
A bangare guda, ministar kudi da kasafin kudi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kashe N118.37 billion annobar Korona kadai a shekarar 2020.
Ministar ta bayyana hakan ne yayin jawabi a taron bayani kan kasafin kudin 2021, ranar Talata, 12 ga Junairu, Vanguard ta ruwaito.
A cewarta, an kashe N10.08 trillion kan gine-gine, biyan basussuka, biyan albashi da fansho da kuma wasu cefane a 2020.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng