Ma'aikatar ilimi ta fitar da sabbin bayanai, NIN ta zama wajibi kafin rijistar JAMB

Ma'aikatar ilimi ta fitar da sabbin bayanai, NIN ta zama wajibi kafin rijistar JAMB

- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu wani dalibi a nan gaba da zai rubuta jarrabawa JAMB ba tare da lambar NIN ba

- A ranar Alhamis ne ministan ilimi Adamu Adamu ya sanar da hakan

- Adamu ya bayyana cewa an umarci hukumar JAMB ta yi aiki tare da hukumar NIMC domin samun nasarar hakan

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga yanzu amfani da lambobin tantancewa na jikin katin dan kasa (NIN) ya zama wajibi wajen rijistar jarrabawar shiga manyan makarantu (JAMB).

Jaridar Nigerian Tribune ta rawaito cewa Ministan ilimi, Adamu Adamu, ne ya sanar da hakan ranar Alhamis yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Ministan ya bayyana cewa ya umarci hukumar JAMB ta yi aiki tare da hukumar bayar da katin dan kasa domin tabbatar da fara aikin sabuwar dokar.

KARANTA: 'Yan bindiga sun sace mataimakin shugaban jami'ar Legas daga kawo yaransa makaranta a arewa

Hukumar JAMB ta so fara amfani da lambar NIN tun shekaru baya da suka gabata, amma hakan bai yiwu ba saboda karancin mutanen da suka mallaki katin shaidar zama dan kasa.

Ma'aikatar ilimi ta fitar da sabbin bayanai, NIN ta zama wajibi kafin rijistar JAMB
Ma'aikatar ilimi ta fitar da sabbin bayanai, NIN ta zama wajibi kafin rijistar JAMB
Source: Twitter

A karshen mako ne kwamitin majalisar wakilai akan harkar ilimi ya bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da batun bude makarantu a ranar 18 ga wata.

KARANTA: Bafarawa ya bayyana dalilin da yasa Buhari ya yi bakin jini wurin shugabannin arewa

A cewar kwamitin, bude makarantu a halin yanzu zai kawo babban nakasu ga yaki da annobar korona a karo na biyu.

Shugaban kwamitin, Honarabul Julius Ihonvbere, ya ce gwamnati bata tuntubi majalisa ba kafin sanar da ranar bude makarantu.

A wani labarin, Legit.ng ta rawaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta cafke mataimakin shugaban makarantar sakandire bisa zarginsa da yi wa daya daga cikin dalibansa ciki.

An kama Malamin mai suna Ibrahim Tukur bayan dalibar da ya yi wa ciki, mai shekaru goma sha biyu, ta haihu amma ta hanyar yi mata tiyatar fitar da jariri.

A ranar Laraba ne rundunar 'yan sanda ta yi holin masu kaifuka daban-daban, cikinsu har da Malam Ibrahim.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel